in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga bangarori daban daban na CAR da su warware sabani ta hanyar shawarwari
2017-03-17 14:17:38 cri

Jiya Alhamis mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana cewa, kamata ya yi bangarori daban-daban na kasar Afirka ta Tsakiya wato CAR, su zama masu hangen nesa, su kuma kara mai da hankali kan moriyar kasar da al'ummarsu.

Haka kuma ya yi kira da su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da juna, ta yadda za su cimma burin tabbatar da zaman lafiya da samun bukasa a kasar lami lafiya.

Wu Haitao ya yi kiran ne yayin budadden taron da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar kan rikicin kasar ta Afirka ta Tsakiya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China