in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Faransa ya ce za a ci gaba da aiwatar da dokar ta baci a fadin kasarsa zuwa 15 ga Yuli
2017-03-17 10:38:10 cri

Jiya Alhamis shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa, wannan rana, wani kayan da aka tura ga ofishin asusun ba da lamuni na kasashen duniya IMF dake kasar ya fashe, haka kuma, an yi harbi da bindiga a wata makarantar midil dake kudu maso gabashin kasar, duk wadannan sun nuna cewa, ya dace a ci gaba da aiwatar da dokar ta baci a fadin kasar har zuwa ranar 15 ga watan Yulin bana.

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ya bayyana cewa, gwamnatin Faransa ta riga ta dauki matakai domin yaki da hadurran da suka faru ba zato ba tsammani, a saboda haka tana fatan al'ummar kasar za su yi hakuri su kai zuciya nesa.

A safiyar jiya, yayin da wani ma'aikacin ofishin asusun ba da lamunin kasashen duniya dake Faransa, ya bude wani kayan da aka turawa ofishin, sai kayan ya fashe, ma'aikacin shi ma ya samu rauni a fuska da hannu, kawo yanzu, hukumar 'yan sandan kasar ba ta bayyana kome ba kan lamarin.

A jiya da rana, an yi harbin bindiga a wata makarantar midil a birnin Glas dake kudu maso gabashin kasar, wasu mutane 4 sun samu raunuka, maharin wani dalibi ne mai shekaru 17, inda tuni aka damke shi.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China