in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya bukaci a tsakaita bude wuta da yin tattaunawar sulhu don kawo karshen yakin Syria
2017-03-16 10:21:06 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya bukaci dukkan bangarori a Syria da su amince da shirin tsakaita bude wuta domin gudanar da tattaunawar sulhu don kawo karshen yakin kasar da ya barke shekaru 6 da suka gabata.

A wata sanarwa ya fitar, Guterres, ya bukaci dukkan bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar da su amince da shirin tsakaita bude wuta karkashin yarjejeniyar da aka amince a lokacin taron birnin Astana, wanda zai ba da damar shigar da kayan agaji, kuma tallafin zai iske dukkan mutanen dake cikin halin bukatar agaji ba tare da sun fuskanci wata matsala ba.

Kana ya bukaci masu fada a ji daga dukkan bangarorin Syriar da su yi kokarin kawar da duk wasu banbance banbance a tsakaninsu domin yin aiki tare don aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta Geneva, da nufin kawo karshen tashin hankalin kasar..

Guterres, ya ce batun rikicin Syria ya shafi duniya baki daya, kuma wajibi ne dukkan bangarori na duniya su hada kai domin aiki tare don kawo karshen rikicin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China