in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 5 a harin kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya
2017-03-16 09:22:25 cri

A jiya Laraba jami'an 'yan sandan tarayyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 5, ciki har da wasu 'yan mata 'yan kunar bakin wake su 4, wadanda suka gamu da ajalinsu a yayin wani harin kunar bakin wake da suka kaddamar a wani kauye dake daura da birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A cewar Damian Chukwu, shugaban hukumar 'yan sandan jihar Borno, maharan, wadanda suka kaddamar da harin a kauyen Usmanti, inda suka kashe wani basaraken kauyen, tare da jikkata mutane16.

Ya ce, mazauna kauyen sun yi yunkurin dakatar da maharani, inda nan take suka tada boma boman dake daure a jikinsu.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar wato NEMA ta ce, tuni ta tura jami'an aikin ceto zuwa wajen da lamarin ya faru ba tare da bata lokaci ba, kuma tuni jami'an suka kammala aikinsu.

Tuni dai jami'an tsaro na yankin suka killace wajen da lamarin ya faru, yayin da 'yan sanda masu kwance boma bomai suke ci gaba da aikinsu a yankin.

Kungiyar Boko Haram, wadda ake zargi da hallaka mutane sama da 20,000, da kuma raba wasu mutanen miliyan 2.3 da muhallansu tun fara kaddamar da hare hare a shekarar 2009, ita ce ake zargi da kai harin na safiyar ranar Laraba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China