in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yakin da ake yi a Syria ya yi mummunan tasiri ga yara
2017-03-14 12:59:12 cri

A wannan Larabar ce yakin da ake yi a kasar Syria, wanda ya barke a shekarar 2011, zai shiga shekara ta 7. Cikin shekarun da suka gabata, yaki ya barnata muhallin kasar, tare da sanya al'ummar kasar, musamman ma yara, cikin matukar akuba.

A jiya Litinin ne, Asusun tallafawa Yara na MDD (UNICEF) ya fitar da wani rahoto, inda ya yi tsokaci kan mummunan tasirin da yakin da aka kwashe shekaru 6 ana gwabzawa a kasar Syria ya haddasawa yaran dake kasar. Inda aka bayyana cewa, tasirinsa ya yi tsanani matuka a shekarar 2016.

Rahotanni ya bayyana cewa, sakamakon karuwar tashin hankali a wurare daban daban na kasar Syria, ana kara samun yaran da aka kashe su ko kuma sanya su zama nakasassu sanadiyar yake-yake, yayin da yaran da aka yi amfani da su a matsayin dakaru su ma sun karu sosai. Bisa alkaluman da Asusun UNICEF ya gabatar, a kalla yara 652 ne aka halaka a kasar Syria a shekarar 2016, adadin da ya karu da kashi 20% bisa na shekarar 2015. Cikin wadannan yara, wasu 255 sun mutu a cikin makarantu, ko kuma a kusa da makarantunsu. Haka zalika, cikin shekarar 2016, an sanya yara fiye da 850 aikin soja, adadin da ya ninka na shekarar 2015. Wasunsu an sa su shiga yaki a fagen daga, yayin da aka kara sanya yara shiga ayyukan ta'addanci. Ayyukan da suka yi sun hada da aikata kisan gilla, da harin kunar bakin wake, ko kuma kula da fursunonin da ake garkuwa da su.

Ban da haka kuma, cututtuka da yanayin kunci da ake ciki suna daga cikin babbar barazanar da yaran kasar Syria suke fuskanta, duk da cewa cututtuka ne na yau da kullum, amma duk da haka yanzu sun zama barazana ga al'umma. A halin da muke ciki kuma, yara miliyan 2 da dubu 800 a kasar Syria suna zama a wuraren da ake fama da matsaloli a fannin jigilar kayayyakin jin kai, yayin da wasu dubu 280 daga cikinsu ke zaune a cikin yankunan da aka yi musu zobe, don haka an kusan katse dukkan hanyoyin da za a iya bi wajen kai musu dauki.

A wani bangare na daban, yaran kasar kimanin miliyan 6 na bukatar samun tallafin jin kai, yayin da miliyoyin yara suka rasa muhallinsu. Yanzu haka akwai yara fiye da miliyan 2 da dubu 300 dake gudun hijira a kasashen Turkiya, da Lebanon, da Jordan, da Masar, da Iraki,. A kokarin ganin sun ci da iyalansu, wasu iyayen sun aurar da 'yayansu ko kuma sun saka su aiki don samun abin da za su rayu. Fiye da kashi 2 bisa kashi 3 na iyalan na bukatar yara su yi aiki a waje sakamakon karancin kudin sayen abinci.

A nasa bangare, Geert Cappelaere, darektan sashin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka na Asusun UNICEF, ya takaita yanayin da yaran kasar Syria suke ciki da cewa, yake-yaken da ake yi a kasar sun yi mummunan tasiri ga lafiyar yara, da zaman rayuwarsu ta yau da kullum, gami da makomarsu a nan gaba.

Bugu da kari, rahoton Asusun UNICEF ya nuna yadda yaran kasar Syria suke sa ran samun rayuwa mai kyau a nan gaba, gami da burin da suke fatan cimmawa. An ruwaito wani yaro mai suna Darcy dake gudun hijira tare da iyalinsa a kasar Turkiya, yana bayyana cewa, yana son zama likita a nan gaba, don ya taimakawa mutane masu fama da cututtuka, da wadanda suka ji raunuka. Ya ce, yana son ganin an kawo karshen yaki a Syria, ta yadda wata rana shi da iyalinsa za su koma gida. Ya ce, yana Allah-Allahr ganin wata duniyar da babu yaki kwata-kwata. Dangane da halayyar yaran Syria, Geert Cappelaere ya ce, yaran suna da jaruntaka, ganin yadda da yawa daga cikinsu suke kokarin halartar jarrabawar da ake yi a makaranta duk da yakin da ake yi a kasar. Suna kokarin karatu, duk da cewa suna cikin makarantar da ke karkashin kasa.

Bisa yanayin kunci da yaran kasar Syria suke ciki ne, Asusun UNICEF ya yi kira ga bangarorin kasar da suke fada da juna, da gamayyar kasa da kasa, da dukkan mutanen da suke kula da yara, da su taimaka don ganin an tsagaita bude wuta a kasar Syria, da daidaita rikici ta hanyar siyasa. Asusun na bukatar dakatar da ayyukan azabtar da yara, da suka hada da kashewa da raunata yara, da shigar da su aiki soja, da kai hari kan asibitoci da makarantu. Haka zalika, asusun ya bukaci a janye zoben da aka yi wa wasu birane, don samar da agaji ga yaran da suke da bukata. Gami da samar da tallafin kudi ga asusun na UNICEF, da gwamnatoci da al'ummomin da suka karbi 'yan gudun hijirar kasar Syria.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China