in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar mulki a Tanzania ta amince da yi wa kundin tsarinta garambawul domin kara masa inganci
2017-03-13 10:05:44 cri

Jami'iyya mai mulkin Tanzania CCM, ta amince da yiwa kundin tsarinta gyaran fuska karo na 16, al'amarin da zai kai ga samar da muhimman sauye-sauye a tsarin jam'iyyar.

Wakilan jam'iyyar 4,000 ne suka amince da batun yiwa kundin tsarin gyaran fuska, yayin taron jam'iyyar da ya gudana jiya karkashin jagorancin shugaban kasar John Magufuli a Dodoma, babban birnin kasar.

A jawabinsa na bude taron, John Magufuli ya ce, manufar sauye-sauyen ita ce, karawa jam'iyyar karfi, ta yadda za ta iya fuskantar jam'iyyar adawa da a yanzu ke kara girma.

Shugaba Magufuli, ya ce yunkurin samar da sauye-sauyen ya samo asali ne daga daddadiyar dabi'ar jam'iyyar ta yi nazarin harkokinta da kanta, yana mai cewa, a nazarin da suka yi bayan babban zaben kasar, sun gano cewa, akwai bukatar aiwatar da wasu gyare-gyare.

Har ila yau, ya ce, sauye-sauyen za su mai da hankali ne ga inganta tsare-tsare da harkokin jam'iyyar, da nufin rage yawan kashe-kashen kudi, baya ga sauran wasu abubuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China