in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta zamo jigo na bunkasar hadin gwiwar kasashe masu tasowa, in ji jami'in MDD
2017-03-10 10:05:28 cri

Wakilin babban magatakardar MDD mai lura da fannin hadin gwiwar kasashe masu tasowa Jorge Chediek, ya ce Sin ta zamo jigo na bunkasar hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, inda ko da a bana, kasar ta shirin karbar bakuncin manyan taruka biyu, na bunkasa wannan hadin gwiwa.

Mr. Chediek, ya ce tarukan hadin gwiwa na tattauna batutuwan da suka shafi shirin nan na ziri daya da hanya daya, da kuma taro na 9, na kungiyar kasashen BRICS, dukkanin su na da alaka da wannan manufa. Ya ce, "Muna daukar shirin ziri daya da hanya daya, a matsayin muhimmin aiki na hada kan kasashe masu tasowa wuri guda, matakin da tuni ya yi matukar tasiri ga kasashe da dama cikin 'yan shekarun nan".

A shekarar 2013 ne dai Sin ta gabatar da shirin ziri daya da hanya daya, wanda ya kunshe wasu muhimman fannonin ci gaba masu tarin yawa, ga kasashen da suka amince su shiga shirin. Za kuma a gudanar da babban taro game da bunkasa wannan manufa cikin watan Mayun wannan shekara a nan birnin Beijing.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China