in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar kasar Koriya ta Kudu sun yi tir da isar na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD a kasar
2017-03-09 11:34:52 cri
A jiya Laraba ne jama'ar jihar Seongju-gun dake Gyeongsangbukdo, da na birnin Gimcheon, wato yankunan da za a girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD, suka gudanar da zanga-zanga a yankunansu, domin nuna adawa da isar na'urorin na THAAD cikin kasar su.

A yammacin ranar, jama'a fiye da dari da suka fito daga wasu kungiyoyin jama'a da dama na Seongju-gun, suka yi zanga-zanga a filin wasan golf na Lotte, inda za a girke na'urorin THAAD din, inda suka yi kira ga gwamnatin Koriya ta Kudu, da ta dakatar da yunkurin girke THAAD ba tare da bata lokaci ba.

Kwamitin yaki da na'urorin THAAD na birnin Gimcheon ya bayyana cewa, kamata ya yi a bi tsarin dokoki na tattaunawa tare da mazauna wurin, da kungiyoyi masu zaman kansu, da kimanta muhalli kafin a girke na'urorin soja, amma gwamnatin ba ta yi haka ba. Maimakon hakan sai kawai ta debo wadannan na'urori na THAAD, bayan ta sa hannu kan yarjejeniyar musayar yanki tare da kamfanin Lotte.

Saboda haka, al'ummar yankin suka yi matukar suka kan wannan mugun aikin, wanda ya yi watsi da ra'ayoyin jama'a, da mahukuntan Koriya ta Kudu da Amurka suka yi.

Kafin wannan, ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Kudu ta tabbatar da cewa, wasu na'urorin THAAD sun riga sun isa sansanin sojan sama na Amurka dake Osan na Koriya ta Kudu, wanda ke da nisan kilomita kimanin 70 daga kudancin Soul, babban birnin kasar.

Kafofin watsa labarun kasar sun ba da labari cewa, sauran na'urori za su isa Koriya ta Kudu a cikin watanni biyu masu zuwa.

Baya ga haka, jaridar Hankyoreh ta Koriya ta Kudu ta bayar da sharhi a ranar 8 ga wata dake cewa, mahukuntan kasashen Koriya ta Kudu da na Amurka, sun inganta aikin jigilar na'urorin THAAD, matakin da sam bai kamata ba, kuma ba su bi dokokin da suka kamata ba. Jaridar ta kuma yi kira da a dakatar da girke na'urorin na THAAD ba tare da wani bata lokaci ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China