in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin MDD dake Rome sun yi kira da a tabbatar da daidaiton jinsi don kawo karshen yunwa da fatara
2017-03-09 10:57:02 cri
Yayin bikin ranar Mata ta duniya a jiya Laraba, shugabannin Hukumomin MDD uku dake Birnin Rome, sun jadadda kudurinsu na kara matse kaimi wajen tallafawa matan karkara, ta yadda za su dogara da kansu, su na masu bayyana matakin a matsayin muhimmin abu da zai kawar da yunwa da fatara.

Hukumomin sun bayyana cewa, a kasashe masu tasowa, kashi 45% na masu aikin gona mata ne, wanda ya hada da kashi 20 daga Latin Amurka zuwa kashi 60 a yankin Afirka da Asia.

Har ila ya, sun ce matan sun fi yin aikin da ba a biya fiye da maza, al'amarin dake yiwa yunkurinsu na samun kudin shiga da fadada basirarsu tarnaki.

Shugabannin sun ce, Saboda wasu dokoki da al'adu dake nuna wariyar jinsi, an raina gudunmuwa da shawarwarin da mata suke bayarwa a fannonin tattalin arziki, siyasa da zamantakewa.

Hukumar abinci da aikin gona ta MDD (FAO) da asusun raya ayyukan gona na duniya (IFAD) da kuma shirin samar da abinci na duniya (WFP), sun kuma tunatar da duniya cewa, mata da 'yan mata na da muhimiyyar rawar takawa wajen cimma muradun cigaba masu dorewa nan zuwa 2030, musammam ma murdin da ake da shi, na kawar da yunwa da matsananciyar fatara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China