Bisa yarjejeniyar da suka cimma, daga watan Janairun bana zuwa karshen watan Yunin bana OPEC za ta rage hako gangunan danyen mai miliyan 1 da dubu 200 a kowace rana, yayin da kasashe 11 masu arzikin mai wadanda ba mambobin kungiyar OPEC ba za su rage hako gangunan danyen mai dubu 558 a kowace rana. (Tasallah Yuan)