in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Girke na'urorin kakkabo makamai masu linzami na THAAD ka iya tsananta halin da ake ciki a zirin Koriya
2017-03-08 12:29:17 cri
Shugaban sashin kula da hana yaduwar makamai na ma'aikatar tsaron kasar Rasha, Mista Mikhail Ulyanov ya bayyana cewa, girke na'urorin kandagarkin makamai masu linzami da ake kira THAAD a kasar Koriya ta Kudu da kasar Amurka ta yi, ka iya tsananta halin da ake ciki a zirin Koriya.

Mista Ulyanov ya bayyana hakan ne jiya Talata a birnin Moscow. Ya ce girke na'urorin THAAD a Koriya ta Kudu, zai iya haddasa takun-saka tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa, abun da zai kuma jawo matukar takaici ga kasar Sin, zai kuma iya haddasa tabarbarewar yanayin tsaro da ake ciki a zirin Koriya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China