Wata sanarwa da rundunar sojan Amurka dake Koriya ta Kudu ta fitar, ta bayyana cewa, za ta ci gaba da aiwatar da kudirin da aka yanke tsakanin kasashen biyu, na girke na'urorin kandagarkin makamai masu linzami samfurin THAAD, da gudanar da wannan aiki ba tare da bata lokaci ba.
Ma'aikatar tsaron Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, a daren jiya Litinin ne, aka aike da wasu na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD sansanin sojojin saman Amurka dake Osan na Koriya ta Kudu, ciki har da na'urorin harba makamai masu linzami guda biyu.
Rahotanni daga kafofin watsa labaran Koriya ta Kudu sun ce, rundunar sojan kasar ta yi shirin kammala aikin shigo da daukacin na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD cikin kasar daga watan Mayu zuwa Yulin bana.(Murtala Zhang)