in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alain Gomis ya lashe babbar kyautar shirya fina finai ta Afirka
2017-03-06 10:24:44 cri
Mashiryin fina finai dan kasar Senegal Alain Formose Gomis, ya lashe babbar kyautar karramawa ta mashirya fim ta nahiyar Afirka. An dai damka lambar yabon ce ta "golden Yennega Stallion" ga Gomis, yayin bikin gamayyar mashirya fina finan nahiyar ko 25 ko "FESPACO", wanda ya gudana a birnin Ouagadougou fadar mulkin kasar Burkina Faso.

Bikin FESPACO dake gudana karo 1 bayan ko wane shekaru 2, na karrama mutanen da suka yi fice a harkokin da suka shafi Sinima da talabijin, an kuma kammala bikin na bana a ranar Asabar, inda Gomis ya zamo zakara, ya kuma karbi lambar yabo da kimar ta ta kai kusan dalar Amurka 32,389. Ya kuma shiga takara ne da fin din sa mai taken "Felicity."

Sauran wadanda ke take masa baya sun hada da Beninese Sylvestre Amoussou a matsayi na 2, yayin da kuma Said Khalaf na Morocco ya zo na 3.

Gomis dai ya taba lashe wannan kyauta shekaru 4 da suka gabata a bikin FESPACO na 23.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China