in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta jaddada muhimmancin kafa makomar dan Adam, yayin da ake kare hakkin dan Adam
2017-03-02 10:32:07 cri

 


Jiya Laraba ne jakada Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD a Geneva da sauran hukumomin duniya dake kasar Switzerland ya ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda ya yi karin bayani kan tunanin kafa makomar dan Adam, muhimmancinsa game da bunkasar aikin kare hakkin dan Adam a duniya, tare da gabatar da ra'ayoyin da suka dace da zamani da kuma bukatun gamayyar duniya.

Jakada Ma Zhaoxu ya ba da wannan sanarwa ce a yayin taron kwamitin kula da harkokin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 34 da ake gudanarwa a birnin Geneva, taron da ya samu wakilcin kasashen duniya 140.

A cikin sanarwar, Ma Zhaoxu ya ce, yanzu haka, ana raya harkokin da bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya bisa matakai. Kasashen duniya suna zaman cude-ni-in-cude-ka, inda suke dogaro da juna, tare da kafa makomarsu baki daya. A sa'i daya kuma, kalubaloli iri daban daban da ake fuskanta suna kawo barazana ga tsaron al'ummar duniya da kuma jin dadin rayuwarsu. Ma ya ce, "A yayin da ake kokarin kiyaye zaman lafiya, da samun ci gaba tare a duniya, da kiyaye da kara azama kan kare hakkin dan Adam, ya kamata kasashen duniya su kafa makomar dan Adam tare, su kafa wata kyakkyawar duniya mai dawamammen zaman lafiya, tsaro, da wadata, tsabta, da kuma kaunar juna."

Don haka, Ma Zhaoxu ya gabatar da ra'ayoyi guda 5, da farko, wajibi ne a tsaya tsayin daka kan yin zaman daidai wa daida a tsakanin dukkan kasashen duniya manya da kanana. Na biyu, wajibi ne a tsaya tsayin daka kan yin tattaunawa da shawarwari dangane da harkokin kare hakkin dan Adam. Na uku kuma, dole ne a tsaya tsayin daka kan yin hadin gwiwar neman samun nasara tare. Na hudu, tilas ne kasashen duniya su tsaya tsayin daka kan yin mu'amala da yin koyi da juna, da girmama al'adu juna. Na biyar kuwa, wajibi ne a tsaya tsayin daka kan samun ci gaba mai dorewa.

A yayin da Ma Zhaoxu yake zantawa da manema labaru bayan jawabinsa, ya nuna cewa, a watan Janairun bana, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi jawabi dangane da kafa makomar dan Adam tare a babban zauren MDD dake Geneva, jawabin da ya samu karbuwa sosai a duniya. A cikin wannan sanarwar da kasashe 140 da kasar Sin suka bayar cikin hadin gwiwa a yayin taron kwamitin kula da harkokin kare hakkin dan Adam na MDD, sun yi kira da a hada kai wajen kafa makomar dan Adam tare, kiyaye da kara azama kan kare hakkin dan Adam, da hada kai tare domin tabbatar da samun bunkasar dan Adam cikin lumana da hadin gwiwar neman samun nasara tare. Mista Ma ya kara da cewa, "Wannan shi ne karo na farko da aka bullo da tunanin kafa makomar dan Adam baki daya" cikin ayyukan kiyaye hakkin dan Adam, wannan lamari yana da muhimmanci matuka. Kasashe 140 ne suke mara wa kasar Sin baya, lamarin da ya nuna cewa, tunanin shugaba Xi ya dace da zamani, wanda kuma ya zo dai-dai da ra'ayin kasashen duniya suka cimma, kuma jama'ar duniya baki daya suna da irin wannan buri. Bisa wannan muhimmin tunani ne za mu hada kai da kasashen duniya wajen ci gaba da bunkasa sha'anin kiyaye hakkin dan Adam, kara kokarin yin hadin gwiwa da mu'amala a tsakanin kasashen duniya ta fuskar kare hakkin dan Adam, da tabbatar da bunkasar sha'anin kare hakkin dan Adam a duniya yadda ya kamata.

A wannan rana, wakilai da dama dake halartar taron sun yi maraba da jawabin jakada Ma Zhaoxu. Jakada Jorge Valero, zaunannen wakilin kasar Venezuela a Geneva, kasar da ke shugabantar kungiyar kasashe 'yan ba-ruwanmu ya bayyana cewa, kungiyarsu ta amince da ra'ayin kasar Sin sosai. Kamata ya yi kasashen duniya su hada kai wajen kafa makomar dan Adam baki daya, inda ya ce, "Muna ganin cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a kwamitin harkokin kare hakkin dan Adam na MDD. Saboda gwamnatin kasar Sin tana tsayawa kan kiyaye 'yancin kowace kasa, da kokarin ganin an bunkasar sha'anin hakkin dan Adam a duniya cikin adalci." (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China