in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya nada sabon firaminista
2017-03-02 10:20:58 cri

Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya nada mataimakin shugaba na farko Bakri Hassan Saleh a matsayin firmainistan kasar.

Wannan ya nuna cewa, Saleh zai ci gaba da rike mukamin mataimakin shugaba na farko, da kuma sabon mukamin firaminista.

Kafin nadinsa a wannan mukami, Saleh ya rike mukaman minista da na siyasa, ciki har da babban jami'in tsaron kasa, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, da ministan cikin gida. Sauran mukaman sun hada da ministan tsaro da minista a fadar shugaban kasa, kafin daga bisani a nada shi mukamin mataimakin shugaba na farko a watan Disamba shekarar 2013.

Babban taron al'ummar kasar ta Sudan da aka kammala a watan Oktoban da ya gabata ne ya amince a bullo da mukamin firaminista. Kana a watan Disamban shekarar da ta gabata majalisar dokokin kasar ta amince da wasu gyare-gyaren da ka yiwa kundin tsarin mulkin kasar, ciki da sabon mukamin na firaminista.

A ranar Talatar da ta gataba ce, kwamitin da aka dorawa alhakin ganin an aiwatar da sakamakon taron ya gana da shugaba al-Bashir, inda ya amince a baiwa jam'iyyar NCP mai mulkin kasar sabon mukamin na firaminista.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China