in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU za ta tura jami'inta Afrika domin kula da batun 'yan ci rani
2017-03-02 10:06:27 cri

Cikin wata sanarwa, hukumar Frontex ta tarayyar Turai mai kula da iyakoki da gabobin ruwan nahiyar, ta ce, a cikin shekarar nan, za ta tura wani jami'i nahiyar Afrika, domin kula da batun kwararar baki.

Sanarwar da hukumar ta fitar jiya, ta ruwaito cewa, jami'in zai kasance a jamhuriyar Nijer, inda zai rika aiki da hukumomin dake tsaron iyakoki domin karfafa hadin gwiwa wajen tsaron iyakokin.

Daraktan zartarwa na hukumar Frontex Fabrice Leggeri ya gana da hukumomin kasar Nijer a cikin wannan makon a Niamey, babban birnin kasar, inda suka tattauna kan hadin gwiwar hukumar da kasashen Afrika.

Ya ce, tsaron iyaka shi ne hanyar magance matsalar 'yan ci rani, yana mai cewa, suna son samar da sabbin hanyoyin karfafa hadin gwiwa tsakanin Frontex da kasashen Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China