in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNSC ta tura wata tawaga zuwa yankin tafkin Chadi
2017-03-02 09:43:11 cri

Yanzu haka wata tawagar kwamitin sulhun MDD tana kan hanyarta ta zuwa yankin tafkin Chadi dake arewa maso tsakiyar nahiyar Afirka. inda za ta shafe mako guda tana tantance irin barazanar da 'yan ta'adda ke yiwa yankin.

Jakadan kasar Burtaniya Matthew Rycroft, kana shugaban kwamitin na wannan wata, shi ne jagoran tawagar. Sauran mambobin tawagar sun hada da jakadun kasashen Faransa Francois DeLattre, da na Senegal Fode Seck. Ana kuma sa ran tawagar za ta gudanar da bincike game da barazanar da kungiyar Boko Haram ta haddasa a kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya.

A jawabinsa ga manema labarai gabanin tashin tawagar, jakadan kasar Faransa DeLattre ya jadadda muhimmancin wannan rangadi, wanda shi ne irinsa na farko da kwamitin sulhun MDD ya shirya zuwa yankin don taimakawa kasashe da ta'addin mayakan Boko Haram ya shafa, kuma yanzu haka suke fuskantar matsalar agajin jin kai.

Ya ce, taken majalisar na wannan wata kamar yadda babban sakatarenta Antonio Guterres ya bayyana, shi ne kare aukuwar tashin hankalin a nahiyar Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China