An rantsar da Amina Mohammed, tsohuwar ministar muhalli ta Nigeria a matsayin mataimakiyar sakatare janar na MDD a jiya Talata.
A jawabinsa na maraba, sakatare janar na majalisar Antonio Guterres ya ce, ya yi matukar farin ciki da ta amince ta yi aiki da shi.
Da take ganawa da manema labarai jiya da safe, Amina Mohammed ta ce, za ta mai da hankali wajen taimakawa sakatare janar din sake fasalin muradun ci gaba masu dorewa a majalisar.
Aikinta na farko shi ne bude sashen majalisar kula da tattalin arziki da zaman takewa na bana, a wani bangare na ayyukan samar da ci gaba.
Amina Mohammed ta kasasnce mace ta biyu 'yar Afrika da aka nada matsayin mataimakiyar sakatare janar na MDD. Mace ta farko ita ce Asha-Rose Migiro, 'yar kasar Tanzania, wadda ta kasance kan mukamin daga 2007 zuwa 2012, karkashin shugabanci Ban Ki-moon. (Fa'iza Mustapha)