in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana kokarin kyautata tsaron abinci
2017-02-28 10:20:28 cri

A jiya Litinin ne, shugaban hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin Bi Jingquan ya bayyana a yayin taron manema labaran da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a nan birnin Beijing cewa, daga sakamakon da aka samu bayan binciken da aka yi kan ingancin abinci a fadin kasuwannin kasar ta Sin, an tabbatar da cewa, duk da cewa, yawancin abinci a kasar Sin suna da inganci, amma bai kai hasashen da al'ummar kasar ke yi ba, shi ya sa gwamnatin kasar Sin za ta kara kokari a cikin wannan sabuwar shekarar da muke ciki domin yaki da laifuffukan da suka shafi tsaron abinci, a kokarin ganin an kare lafiyar al'ummar kasar yadda ya kamata.

A yayin taron watsa labaran da aka gudanar a jiya Litinin, shugaban hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin Bi Jingquan ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, yanayin tsaron abincin da kasar Sin ke ciki yana da kyau, kuma yana kara kyautatuwa. Yana mai cewa, "Yanzu muna cike da imani kan ingancin abinci a kasarmu, dalilin da ya sa haka shi ne domin sakamakon binciken da muka samu ya nuna cewa, akwai ingancin abinci a fadin kasar. A shekarar 2016 da ta gabata, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin ta gudanar da bincike kan abinci iri iri har sau dubu 257, kuma adadin abincin da ya kai ma'aunin ingancin kasa ya kai kaso 96.8 bisa dari, sakamakon da ya yi daidai da na shekarar 2015, amma adadin ya karu da kaso 2.1 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2014. Kana hukumar ta yi bincike kan wasu manyan kamfanonin samar da abinci da yawansu ya kai sama da 1300, daga baya an samu sakamakon cewa, adadin abincin da ya kai ma'aunin ingancin kasa ya kai kaso 99 bisa dari, ban da haka kuma, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ba a gamu da hadarin tsaron abinci mai tsanani a nan kasar ta Sin ba."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin kasar Sin tana kara mai da hankali kan aikin kula da ingancin abinci, a shekarar 2016, gwamnati ta fitar da wasu sabbin manufofi 530 game da tsaron abinci, wadanda ke shafar ma'aunin tsaron abinci kusan dubu 20, a cikinsu, har da sabbin ma'aunin sinadaran da aka amfani da su a cikin abinci, bayan da aka gano an yi amfani da takin zamanin a cikin abinci, kana an gudanar da bincike kan abinci har sau dubu 257, adadin da ya karu da kaso 50 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2015. A sa'i daya kuma, a ko wane mako, sassan dake aikin sanya ido kan ingancin abinci da magunguna na kasar Sin su kan sanar da sakamakon da suka samu bayan da suka gudanar da bincike kan abinci, kuma sun dauki matakan hana sayar da kayayyakin da ba su kai ma'aunin inganci ba domin magance aukuwar duk wani hadari. Kazalika, a bara, adadin laifuffukan da suka shafi tsaron abinci ya kai dubu 170, adadin laifuffukan da hukumar kiyaye kwanciyar hankalin jama'a ta kasar ta hukunta ya kai dubu 11, hakan ya taimaka matuka wajen hana aikata laifuffuka a wannan fannin.

Duk da cewa, an samu sakamako a bayyane, amma Bi Jingquan ya jaddada cewa, ana fuskantar matsala yayin da ake kyautata tsaron abinci a kasar Sin, ya ce, "Kasar Sin tana da yawan al'umma, kuma ba ta samu ci gaba cikin sauri ba tukuna, shi ya sa ake fuskantar matsala a fannin kiyaye tsaron abinci, shi ya sa aikin bai kai hasashen da al'ummar kasar ke yi ba, misali hadarin da ake fama wajen tsaron abinci sakamakon amfani da takin zamani da kuma maganin da dabbobin suka sha, da hadarin da ake fuskanta a fannin saboda dalilin kazantar muhalli, da hadarin da ake gamuwa yayin da ake jigila da kuma adana da abinci da dai sauransu. Ban da haka wasu 'yan kasuwa su kan hada abubuwa a cikin abinci ba bisa ka'ida ba."

Bi Jingquan ya ci gaba da cewa, a cikin sabuwar shekarar da muke ciki, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin za ta kara daukar matakai domin yaki da kuma shawo kan hadurran dake shafar tsaron abinci, tare kuma da yaki da laifuffukan hada da kuma sayar da magungunan jabu, yana mai cewa, "Za mu kara kokari domin kyautata aikinmu na tabbatar da tsaron abinci, wajibi ne a nace ga nuna ba sani ba sabo game da batun yaki da laifuffukan tsaron abinci. Babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya taba bukatar mu da mu kara ba da muhimmanci kan aikin tabbatar da tsaron abinci, a saboda haka za mu ci gaba da daukar matakai domin kiyaye lafiyar al'umma yadda ya kamata."

Bi Jingquan ya jaddada cewa, nan gaba za a kara karfafa aikin sanya ido kan tsaron abinci, musamman ma a dakin cin abinci na makarantu, da liyafar da aka shirya domin taya murna a kauyuka, da dakin cin abinci a wuraren shakatawa, da abincin da aka shirya domin fasinjojin jirgin kasa, ta yadda za a hana aukuwar hadarin tsaron abincin dake shafar jama'a da dama.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China