in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mene ne hujjar Trump na ganin Amurka ta mallaki karin makaman nukiliya?
2017-02-27 13:28:40 cri

A kwanakin baya ne, shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya nuna matukar takaicinsa game da yarjejeniyar takaita mallakar makaman nukiliya da aka daddale tsakanin Amurka da Rasha, inda ya ce, zai yi kokarin ganin kasarsa ta mallaki karin makaman nukiliya. Tun bayan da ya dare karagar mulkin kasar Amurka, Trump ba ya sassautawa kasar ta Rasha, kuma maganarsa ta ganin Amurka mallaki karin makaman nukiliya ta sa Rasha ta farka daga barcin da take yi. Kwararru na ganin cewa, idan gwamnatin Trump ba ta ci gaba da martaba manufofin da suka shafi mallakar makaman nukiliya tsakaninta da Rasha kamar yadda gwamnatocin da suka gabace shi suka aiwatar ba, hakan ka iya sake haifar da gasar mallakar makamai tsakanin Amurka da Rasha. Abokin aikinmu Murtala yana dauke da karin bayani.

Kwanan baya, yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Donald Trump ya ce, yarjejeniyar ragewa gami da takaita mallakar makaman nukiliya da aka cimma tsakanin Amurka da Rasha a shekara ta 2010, ba ta je ko'ina ba, wato yarjejeniyar da aka daddale kan batun nukiliya na Iran, ita ce mummunar yarjejeniyar da Amurka ta rattaba hannu a kai. Trump ya ce, idan Amurka na son zama kan gaba ta fuskar nukiliya, dole ne ta kara mallakar makaman nukiliya. Ya kuma kara da cewa, a duk lokacin da ya gana tare da takwaransa na Rasha, wato Vladimir Putin, zai bayyana ra'ayinsa game da sabawa yarjejeniyar amfani da makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango da Rasha ta yi.

Rasha da Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ragewa gami da takaita amfani da makaman nukiliya a shekara ta 2010, inda aka tanadi cewa, kasashen biyu su rage yawan makaman nukiliyar da suke da su. Ana kallon wannan yarjejeniya a matsayin wani tushe na yin amfani da makaman nukiliya cikin ruwan sanyi, wadda wa'adinta zai cika a shekara ta 2021.

Amma, kalaman da Trump ya yi, wato yunkurin ganin Amurka ta kara mallakar makaman nukiliya, sun jawo damuwa sosai a cikin kasar Rasha. Shugaban kwamitin kula da harkokin kasa da kasa na majalisar wakilan Rasha Leonid Slutsky ya ce, idan Amurka ta ci gaba da yunkurinta na kara mallakar makaman nukiliya, tabbas za a samu gasar mallakar makamai, kuma yakin cacar baki zai sake aukuwa a fadin duniya.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin kula da harkokin tsaro na majalisar dattawan Rasha Viktor Ozerov ya nuna cewa, Rasha ta ki yarda da dakatar da amfani da yarjejeniyar ragewa gami da takaita mallakar makaman nukiliya, har ma Rasha na fatan tsawaita wa'adin yarjejeniyar.

Shi kuma Mitsa Yury Baluyevsky, kana tsohon babban hafsan hafsoshin sojan Rasha, ya ce, idan Amurka ta kara mallakar makaman nukiliya, Rasha za ta mayar da martani, na kara yawan makamanta na nukiliya domin tinkarar barazana daga Amurka.

Manazarta suna ganin cewa, Trump ya yi wadannan kalamai na ganin Amurka ta kara mallakar makaman nukiliya don tinkarar Rasha, ta yadda zai karfafa tushen tafiyar da mulkin shugabancin Amurka. Trump yana tsammanin cewa, idan gwamnatinsa ba ta daidaita matsayinta kan Rasha ba, to za ta iya fuskantar karin kalubale mai tsanani.

Mataimakin shehun malami a cibiyar nazarin manyan tsare-tsaren kasa da kasa ta makarantar koyon ilimin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mista Liang Yabin ya ce, tun lokacin da Trump ya hau karagar mulkin kasar Amurka, gwamnatinsa take fuskantar bakin jini daga sassa daban-daban daga cikin gida da wajen kasar. Har wa yau kuma, yayin da yake yakin neman zabe, Trump ya yi furucin kara daukaka Amurka, wannan 'daukaka' ba ma kawai ta bayyana ta fannin tattalin arziki ba, har ma ta fannin aikin soja. Saboda haka, ra'ayin da Trump ya nuna, wato Amurka ta kara mallakar makaman nukiliya, wani mataki ne da ya dauka na tinkarar halin da yake ciki yanzu, kana wani mataki ne na cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabensa.

Sai dai kuma wasu kafofin watsa labaran duniya na ganin cewa, sabbin kalaman da Donald Trump ya yi game da batun nukiliya sun nuna cewa, akwai yiwuwar sake bullar takarar mallakar makamai tsakanin Amurka da Rasha, al'amarin da zai kara dagula dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A cewar Liang Yabin, a hakika, Amurka da Rasha sun riga sun fara rige-rigen mallakar makamai a yankin gabashin Turai. Kwanakin baya, sanata John McCain ya zargi kasar Rasha saboda wasu ayyukanta wadanda suka sabawa yarjejeniyar amfani da makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango, haka kuma kungiyar NATO ta fara girka dakarunta a gabashin Turai, ciki har da tura sojoji zuwa kasashen Poland da Lithuania. Don haka ana tsammanin cewa, dangantakar dake tsakanin Amurka da Rasha za ta kara dagulewa, wata kila ma lamarin ya tsananta.

Wasu kwararru na nuna cewa, kasashen Rasha da Amurka suna iya sassauci a wasu bangarori na dangantakar dake tsakaninsu, amma ba za'a iya kyautata dangantakar daga tushe ba, kuma kasashen biyu za su ci gaba da ja-in-ja a fannonin da suka shafi batun nukiliya, da na'urorin kakkabo makamai masu linzani, gami da rikicin kasar Ukraine. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China