Shugaban kungiyar ta FESPACO Bakupa Kanyinda ya bayyana cewa, an kebe sefa miliyan 3, kwatankwacin dalar Amurka 4,830 don tunawa da marigayi Thomas Sankara, mutumin da ya jagoranci kasar Burkina Faso a shekarun 1980.
Tun a ranar Asabar din da ta gabata ce kungiyar ta fara taronta na 25 a birnin Ouagadougou na kasar ta Burkina Faso. Kungiyar dai tana daukar marigayi Thomas Sankara mutumin da aka kashe shi a wani juyin mulkin soja a watan Oktoban shekarar 1987, kana daga bisani shugaba Blaise Compaore ya daure karagar mulkin kasar, a matsayin jagoran juyin juya hali.
Kimanin kamfanonin shirya fina-finai 150 ne za su fafata a wannan biki, inda 20 daga cikinsu ke neman lashe babbar lambar yabo ta gasar mai suna "Stallion of Yennega". A ranar 4 ga watan Maris ne ake sa ran rufe bikin. (Ibrahim)