in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daga darajar Naira, shin za a samu dorewar sabon tsarin babban bankin Nijeriya?
2017-02-26 13:28:10 cri

Babban bankin Nijeriya ya sauya tsarin sayar da kudaden ketare ta hanyar sayarwa bankuna kudaden, a wani yunkuri na daga darajar takardar Naira da ke saurin faduwa.

Karkashin sabon tsarin da aka kaddamar ranar Talata da ta gabata, bankin ya samarwa da bankunan kasuwanci 23 Dala miliyan 370.9 domin ragewa 'yan Nijeriya matsalar musayar kudaden ketare.

Kakakin babban bankin CBN, Isaac Okorafor ya ce a shirye bankin ya ke ya taimakawa bankuna, ta hanyar tabbatar da ba a samu sauyawar farashi ba da kuma tsare gaskiya, ta yadda za a samu ingantaccen tsarin musayar kudaden ketare.

A cewarsa, an mikawa bankunan dala miliyan dari biyar don saye, amma kuma duk cikinsu babu wanda ke da kwatankwacin kudin a takardar Naira.

Da wannan sabon mataki, a yanzu, hankalin al'ummar kasar masu amfani da Dalar zai kwanta, ganin cewa za a yanzu za su iya samu kai tsaye daga bankuna domin amfaninsu ciki har da tafiye-tafiye, biyan kudin asibiti da na makaranta a kasashen waje da dai sauransu.

Amma tambayar a nan ita ce, ta yaya za a tabbatar da dorewar sabon tsarin bankin? Domin ya na iya rushewa a kokarin da ake na magance kalubalen da ya addabi tattalin arzikin kasar da kasuwar musayar kudi.

Cikin shekaru biyu da suka gabata, tsananin bukatar takardar Dala a Nijeriya ya sa darajar Naira ta ragu, a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki.

Darajar Naira ta fara faduwa ne a shekarar 2014, biyo bayan raguwar kudin shiga da kasar ke samu daga man fetur, saboda faduwar farashin mai a kasuwar duniya.

Da farko, a watan Nuwamban 2014, a kokarinsa na daidaita al'amura, sai da babban bankin ya rage darajar naira, inda aka yi musayar Dala daya a kan Naira dari da saba'in da shida, maimakon Naira dari da sitttin da yake a baya.

Haka zalika a watan Fabrerun 2015, bankin ya sake daukar wani mataki, inda ya dakatar da sayarwa da bankuna Dalar, ya kuma mayar da farashin Dala daya zuwa Naira dari da casa'in da shida da digo biyar, daga baya kuma ya kara mayarwa zuwa Naira dari da casa'in da bakwai.

A ranar 23 ga watan Fabrerun, babban bankin ya cire wasu bangarori na cikin gida daga cikin jerin wadanda ake ba Dalar, a wani yunkuri na inganta sarrafa kayayyaki a cikin gida.

Matsalar rashin dalar ta ci gaba da yin mummunan tasiri a kasuwar bayan fage, da farko darajar Nairar ta fadi, inda ake canza Dala akan Naira dari biyu da arba'in, inda farashin ya ci gaba da sauyawa, har ya kai Naira dari biyar da ashirin da yammacin ranar Litinin din da ta gabata, gabanin sanar da sabon tsarin.

Domin tabbatar da dorewar sabon tsarin, babban bankin zai fara sayarwa bankunan kasuwanci 21 dala miliyan daya a kowacce rana akan Naira dari uku da saba'in da biyar domin samar da shi ga masu bukata da kuma daidaita farashin da na kasuwar bayan fage.

Sai dai, yanayin kasuwar musayar kudin ne kadai zai tabbatar da dorewar sabon tsarin.

A ranar 19 ga watan Oktoban 2016, asusun ajiyar Nijeriya na ketare ya karu zuwa dala biliyan 27.4 daga Dala biliyan 23.8 da ya kasasnce a ranar 19 ga watan Junairun 2015.

Wani masanin harkokin kudi, ya ce dorewar sabon tsarin abu ne mai wahala, duba da yadda darajar takardar Naira ke saurin faduwa.

Sherffdeen Tella, Shehun Malami a sashen nazarin tattalin arziki na Jami'ar Olabisi Onabanjo dake Ogun a yanki kudu maso yammacin Nijeriya, ya ce bai yadda cewa sabon tsarin ba zai zuke asusun ajiyar Nijeriya na ketare ba ko kuma kara ta'azzara kalubalen musayar kudade.

Ya ce duk da manufar tsarin, ba mataki ne da zai magance matsalar da ake ciki ba, a don haka, zai iya janyowa bankin babbar matsala.

Ya kara da cewa, 'yan Nijeriya ciki har da bankunan kasuwanci, za su yi amfani da damar wajen sayan dalar daga Babban bankin su kuma sayar a kasuwar bayan fage.

Dake tabbatar da sabon tsarin zai bunkasa ayyukan masana'antu, shugaban Kungiyar masu masana'antu ta Nijeriya na jihar Ogun, Wale Adegbite, ya ce sabon tsarin zai saukakawa 'yan Nijeriya wahalar samun kudaden ketare.

Ya ce wadatuwar Dala zai ba masu masana'antu damar fara aiki.

Shi ma Johnson Chukwu, masani kan harkokin kudi, ya bayyana aiwatar da tsarin a matsayin fadada wani tsari da dama akwai shi.

Duk da ya yabawa bankin bisa yunkurinta, ya bayyana shakku kan dorewar tsarin.

Shi kuwa, wani kwararren kan hada-hadar kudade Emanuel Ukeje, ya tabbatar da cewa tsarin mai dorewa ne, ya na mai bayanin cewa, zai magance matsalar boye dalar da ake yi, tun da za a iya biyan kudin makaranta ko na asibiti a kasashen waje kai tsaye daga bankuna.

Ukeje wanda mashawarci ne ga Gwamnan babban bankin, ya tabbatar da cewa, bankuna za su yi biyayya ga sabon tsarin ba wai mai da shi mai wahala da zai sake mai da jama'a kasuwar bayan fage ba.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China