in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kawancen majalisun dokokin kasa da kasa ya yi kira da a dauki matakan magance yaduwar bala'in yunwa a Afirka
2017-02-24 13:00:08 cri

A jiya Alhamis ne kawancen majalisun dokokin kasashe daban daban, ya bayar da sanarwa a babbar hedkwatarsa da ke Geneva, inda ya yi kira da a dauki matakan gaggawa, domin magance yaduwar bala'in yunwa da ake fama da shi a arewa maso gabashin Najeriya, da kuma kasashen da ke kuryar Afirka.

Sanarwar ta ruwaito babban sakataren kawancen Martin Chungong na cewa, ya kamata gamayyar kasashen duniya su hada gwiwa da juna, wajen hana yaduwar bala'in yunwa, a kokarin magance karuwar mutane masu dimbin yawa da yunwar ka iya hallakawa.

Bugu da kari, Mr. Martin ya furta cewa, yawancin kasashen da batun ya shafa suna fama da bala'in ne sakamakon dalilin wasu ayyuka na bil Adama, don haka ya kamata gwamnatocin kasashen su yi kokarin neman samun hanyar warware wannan rikici, da kuma ba da tabbaci ga samar da taimakon jin kai zuwa ga wadanda suke da matukar bukatarsa.

Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a ranar 22 ga watan nan cewa, akwai mutane fiye da miliyan 20 da ke kasashen Najeriya, da Sudan ta Kudu, da Somaliya, da kuma Yemen da ke fama da bala'in yunwa, ana kuma bukatar kudi da yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 4.4 domin ba su taimakon gaggawa. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China