in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana ilimin sararin samaniya sun gano wasu duniyoyi 7 kusa da duniyar wata
2017-02-23 10:54:27 cri

Masana ilimin sararin samaniya sun ce, sun gano wasu duniyoyi 7 da ke kewaya wani tauraro mai nisan tafiyar shekarun haske 40 daga duniyar bil'adama, wadanda kuma ke da yanayin da dan Adam ka iya rayuwa a cikin su.

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ce ta tabbatar da gano duniyoyin, yayin wani taron manema labaran da ya gudana a jiya Laraba.

Da yake karin haske game da hakan, kusa a hukumar ta NASA Thomas Zurbuchen, ya ce an yi amfani da wasu madubai na hangen nesa masu tsananin karfi, wajen cimma nasarar wannan aiki. Ya ce, wadannan duniyoyi na kusa da duniyar bil Adama, suna kuma kunshe da ruwa da duwatsu, wadanda ke alamta yiwuwar rayuwa a cikin su.

Nasarar wannan bincike dai ta kafa wani sabon tarihi, na karuwar adadi mai yawa, na duniyoyin da bil Adama ka iya rayuwa a cikin su, wadanda ke kewaye da duniyar wata, a kuma wajen da'idar duniyar mu, kamar dai yadda hukumar ta NASA ta bayyana.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China