in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane miliyan 20 na cikin halin yunwa a kasashe 4
2017-02-23 10:20:46 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya ce, sama da mutane miliyan ashirin ne ke fuskantar matsananciyar yunwa a kasashen Sudan ta Kudu da Somalia da Yemen da kuma arewa maso gabashin Nijeriya.

Da yake ganawa da manema labarai jiya Laraba, Guterres ya ce, ayyukan jin kai a kasashen hudu, na bukatar sama da dala biliyan 5.6 a bana, kuma ana bukatar a kalla dala biliyan 4.4 zuwa karshen watan Maris domin magance matsalar.

A cewar Guterres, domin magance kara ta'azarrar yanayin, akwai bukatar MDD ta kara inganta ayyukan jin kai a kasashen hudu ta hanyar kai abinci da sinadaran gina jiki, sai dai rashin isasun kudaden ya kasance babbar matsala a gare ta.

Baya ga samar da kudade, Guterres ya nemi a sake tsarin hadin gwiwa tsakanin hukumar raya kasashe da hukumar ba da agajin jin kai ta MDD, ta yadda za a samar da dabarun kai dauki mai nisan zango.

Har ila yau, ya ce za a kafa wani kwamitin da zai kunshi jami'an hukumar raya kasashe da na sauran hukumomin MDD domin inganta harkokin agajin jin kai. ( Fa'iza Mustapha )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China