in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya gana da firaministan kasar Faransa
2017-02-22 20:40:52 cri

A yau Laraba ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Faransa Bernard Cazeneuve a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya nuna cewa, kasashen Sin da Faransa abokai ne bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kana su zaunannen mambobi ne a kwamitin sulhun MDD. Saboda haka, bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, ya dace da babbar moriyar jama'arsu, kuma zai taimaka ga ci gaban duniya baki daya.

Baya ga haka Xi ya nuna cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Faransa su karfafa hadin kai game da harkokin da suka shafi duniya, da kiyaye manyan ka'idojin dangantakar duniya, da yaki da ra'ayin ba da kariyar cinikayya, da kuma inganta ayyukan yin kwaskwarima ga harkokin kasa da kasa. Kasar Sin ma na goyon bayan yunkurin dunkulewar Turai, tana mai fatan ciyar da dangantakar abokantaka a tsakaninta da kasashen Turai.

A nasa bangaren, firaminista Cazeneuve ya bayyana cewa, kasarsa na kokarin inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin ta da Sin. A cewarsa, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a kan harkokin duniya, za kuma ta ci gaba da kokarin ciyar da dangantakar dake tsakanin Turai da Sin gaba bisa tushen amincewa da juna.

Shi ma shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya gana da firaminista Cazeneuve a wannan rana.(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China