in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a nace ga ka'idar warware batun Syria ta hanyar siyasa
2017-02-22 10:01:28 cri

Za a gudanar da wani sabon zagaye na shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar Syria, tun daga gobe Laraba 23 ga watan nan a kasar Switzerland.

Kafin hakan, manzon musamman na gwamnatin kasar Sin kan batun Syria Xie Xiaoyan, ya kai ziyara ta yini daya a kasar Iran a jiya Litinin, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi a nace ga ka'idar warware batun Syria ta hanyar siyasa.

A jiya Litinin 21 ga wata, yayin da manzon musamman na kasar Sin Xie Xiaoyan ke ziyara a kasar Iran, ya tattauna da wasu manyan jami'an diplomasiyya na kasar, game da wasu batutuwan da suka shafi yanayin da Syria ke ciki, da shawarwarin wanzar da zaman lafiya a Syria da za a gudanar a Geneva, inda suka yi musanyar ra'ayoyi tsakaninsu. Kafin shawarwarin, Xie Xiaoyan ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan sassa daban daban da za su halarci shawarwarin Geneva, za su yi hakuri bisa tushen fahimtar juna, domin warware batun Syria ta hanyar siyasa, tare kuma da cimma burin tsagaita bude wuta a kasar daga duk fannoni. "Kan batun Syria, kasar Sin ba ta mai da hankali kan moriyar kanta ko kadan, fatan ta kawai shi ne a kara kaimi wajen ganin an cimma burin wanzar da zaman lafiya a kasar, kana kasar Sin tana da ra'ayoyi guda uku game da hakan, na farko dai shi ne tana fatan za a ci gaba da kokarin gudanar da shawarwarin zaman lafiya. Na biyu kuma wajibi ne a nace ga ka'idar warware batun Syria ta hanyar siyasa. Sai na uku, wato kasar Sin tana ganin cewa, ya kamata al'ummar kasar Syria su daidaita batun kasar su da kansu, wato ya fi dacewa a cimma burin wanzar da zaman lafiya a kasar, ta hanyar tabbatar da sulhu tsakanin sassan dake gwabzawa da juna a kasar ta Syria."

Xie Xiaoyan ya kara da cewa, kafin wannan, yanayin siyasa da Syria ke ciki ya riga ya samu kyautatuwa. Misali, rundunar sojojin gwamnatin kasar, da dakarun dake adawa da gwamnatin sun daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta, karkashin shiga tsakani na wasu kasashen duniya kamar Rasha, kana kasashe uku wato Rasha, da Iran, da Turkiyya, sun kafa tsarin sa ido kan tsagaita bude wuta. Ban da haka kuma, kasashen uku sun gudanar da shawarwari a Astana domin daidaita batun Syria har sau biyu. Duk wadannan suna da babbar ma'ana yayin da ake kokarin warware batun Syria ta hanyar siyasa.

Xie Xiaoyan ya kuma jinjinawa shawarwarin zaman lafiya da kasashen Rasha da Iran da Turkiyya suka yi a Astana, inda ya bayyana cewa, "An gudanar da shawarwarin Astana ne duba da cewa, ba a samu sakamako yayin shawarwari da dama da aka yi a Geneva ba, musamman ma a karo na uku, inda aka rika cin karo da matsala. Don haka cikin sauki ana iya ganin ma'anar taron Astana, wato gwamnatin kasar Syria da dakarun adawa suka yi shawarwari kai tsaye, inda aka sake maido da shawarwarin zaman lafiya tsakanin sassan biyu. Ko shakka babu wannan babban ci gaba ne da aka samu, zai kuma taka rawa wajen ingiza wanzar da zaman lafiya a kasar."

Xie Xiaoyan ya kara da cewa, Rasha ta taba bayyana cewa, taron Astana zai taimakawa taron Geneva karkashin jagorancin MDD, yayin da ake warware batun Syria. Xie Xiaoyan shi ma ya jaddada cewa, rawar da MDD take takawa, yayin da ake gudanar da shawarwarin zaman lafiya a Geneva na da muhimmanci matuka, kuma kamata ya yi a kara karfafa hakan.

Duk da cewa, a halin da ake ciki yanzu, yanayin da Syria ke ciki ya kyautata, kuma za a gudanar da shawarwarin zaman lafiya kan batun Syria karo na 4 a Geneva, a hannu guda Mr. Xie Xiaoyan bayyana cewa, batun Syria batu ne mai matukar sarkakiya wanda bai taba gamuwa da irin sa a tarihin aikinsa na diplomasiyya a tsawon shekaru sama da 30 ba. Ya ce, ba zai yiyu a warware batun Syria cikin gajeren lokaci ba. Sai dai ana bukatar sassan da abin ya shafa su ci gaba da kokari tare, ta yadda za a kai ga warware matsalar bisa matakai daban daban. Xie Xiaoyan yana mai cewa, "Ba zai yiyu a warware irin wannan matsala mai sarkakiya cikin gajeren lokaci ba, ko ma ta hanyar gudanar da shawarwarin zaman lafiya sau daya ko sau biyu ba, amma bai dace mu rasa imanin samun nasara yayin da muke cin karo da matsaloli ba. Kamata ya yi mu yi hakuri, mu kara kokari, mu kara amfani da lokaci, da haka za mu kai ga warware wannan matsala ta hanyar siyasa yadda ya kamata. Muna cike da imanin cewa, za a iya kaiwa ga warware matsalar nan wata rana. Duk da cewa ba yanzu nan take ba, ko kuma a ce ba abu ne mai sauki a iya warware batun Syria a yayin taron da za a gudanar a Geneva ba, amma tabbas za a iya cimma wannan buri, idan muka ci gaba da kokari tare."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China