Mista Lapaque ya yi wannan furuci ne a shekaran jiya Litinin, yayin taron kara wa juna sani kan batun kandagarki, da kawar da jarabar shan kwaya a yammacin Afirka, wanda ya gudana a birnin Abijan, fadar mulkin kasar Ivory Coast. Ya ce a baya yankin yammacin Afirka ya kasance yanki da masu jigilar miyagun kwayoyi ke amfani da shi wajen safarar kwayoyin, amma a shekarun baya bayan nan, yankin ya fara zama wuri da ake sarrafa kwayoyin tare da amfani da su. (Bello Wang)