in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Turai da Amurka na kokarin cimma matsaya daya kan tsaron kasashen duniya
2017-02-20 10:54:04 cri

A ran Asabar da ta gabata, wato 18 ga watan nan, yayin da aka shiga rana ta biyu ta taron tsaro na birnin Munich karo na 53, shugabar gwamnatin kasar Jamus madam Angela Merkel, da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence sun halarci zaman, inda kuma a karon farko, madam Angela Merkel ta gana da mambobin sabuwar gwamnatin kasar Amurka.

Da safiyar wannan rana, madam Merkel, da Mr. Mike Pence, da Mr. babban sakataren MDD Antonio Guterres, da babban sakataren kungiyar NATO Mr. Jens Stoltenberg, da kuma babbar wakiliyar kawancen EU wadda ke kula da harkokin waje da manufofin tsaron madam Federica Mogherini, daya baya daya ne suka gabatar da jawabai bisa jigon "dangantakar abokantaka dake ketare tekun Atlantika, da odar kasashen duniya".

A cikin jawabinta, madam Merkel ta ce, a cikin shekaru da yawa da suka gabata, duniyarmu ta samu sauye-sauye matuka. Kuma dangantakar dake tsakanin manyan kasashen duniya, da halin siyasa da ake ciki a wasu muhimman yankuna, da kuma odar kasashen duniya dukkansu sun shiga sabon yanayi. Bisa wannan sabon halin da ake ciki, babu wata kasa za ta iya tunkarar kalubale ita kadai. "Alal misali, batun yakar ta'addanci na masu tsattsauran ra'ayin Islama, ba yaki ne da za a iya dogaro kan al'ummar Turai kawai ba, idan har ana son cin nasararsa. Muna bukatar karfin sojan kasar Amurka. Sakamakon haka, hadin gwiwa tsakanin kasashen Turai da Amurka yana da muhimmanci matuka. A waje daya kuma, ya kamata kasashen Turai su fi mai da hankulansu kan wasu muhimman batutuwa, kamar su karfin yin takara, da samar da guraben aikin yi, da tsaron kai da dai makamantansu, musamman ma ya kamata su zuba karin kudi wajen tsaron kansu. Ko shakka babu, ina da imanin cewa, tabbas matakan tsaron kai na kasashen Turai za su ba da taimako ne kawai, ba wai maye gurbin ka'idojin tsaron kai na kungiyar NATO ba."

A nasa bangare kuma, Mr. Mike Pence, mataimakin shugaban kasar Amurka ya jaddada cewa, "A yau, a madadin shugaba Donald Trump, na alkawarta cewa, kasar Amurka za ta ci gaba da tallafawa kungiyar NATO, kuma za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen cika alkawarin da ta yi wa kawancen ketare tekun Atlantika. Makomar kasar Amurka da ta kasashen Turai na kasancewa iri daya, matsalolin da kuke fuskanta su matsalolinmu ne, kuma ci gaban da kuka samu kamar ci gaban mu ne. Daga karshe, za mu samu ci gaba tare. Wannan alkawari ne da shugaba Donald Trump ya yi muku."

Sannan, a lokacin da yake jawabi, Mr. Antonio Guterres ya nuna cewa, a lokacin da ake ambato batun tsaron kasashen duniya, tabbas ne za a ambaci batun bunkasa duk duniya bai daya. A hakika dai, kokarin bunkasa duk duniya bai daya na kyautata zaman rayuwar al'ummomi, amma a lokacin da ake samu arziki a duk duniya, ana kuma fuskantar kalubalolin rashin tsaro da kwanciyar hankali, sakamakon karuwar gibi da rashin adalci dake kasancewa tsakanin masu arziki da talakawa. "Yanzu haka akwai rikice-rikice da yawa da muke bukatar warware su. Amma a ganina, bai kamata a kyale wani abu ba, wato za a gamu da sabuwar matsala a nan gaba kan batun tsaron kai. Dole ne yanzu mu yi aikin share fagen tinkarar hakan."

Bugu da kari, a ganin babban sakataren kungiyar NATO Jens Stoltenberg, ana da muhimmin nauyi na tabbatar da kwanciyar hankali, da kuma tinkarar ayyukan ta'addanci a yankin Turai. Ya ce, a lokacin da ake kara tsaron kai bisa karfin kungiyar karkashin inuwar tallafin kasar Amurka, wani abu da ya fi muhimmanci shi ne, kowace mambar kawancen ta sauke nauyin dake bisa wuyanta bisa ka'idar nuna adalci, da zaman daidaito. Mr. Jens Stoltenberg ya nuna cewa, "Hadin kai ne da ya sa kungiyar NATO ta samu karfi. Ko da yake akwai ra'ayoyi daban daban a tsakaninmu, hakan ba abu ne da ke iya haifar da tsoro ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, shugabannin gwamnatocin kasashen dake ketaren tekun Atlantika, su iya cimma matsaya daya kan muhimman ayyukan da ya kamata su yi, wato na tsaron juna, da neman 'yanci, da kuma tsaron tunaninmu."

Sannan, a cikin jawabinta, babbar wakiliyar kawancen kasashen Turai mai kula da harkokin waje da manufofin tsaron kai madam Federica Mogherini, ta nuna imani sosai ga makomar kungiyar EU. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China