in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres: Samun ci gaba muhimmiyar hanya ce ta rigakafin riciki
2017-02-19 13:38:58 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana a jiya Asabar a birnin Munich cewa, bisa yanayi mai tsanani da duniya ke ciki, neman ci gaba ya kasance muhimmiyar hanya ta rigakafin barkewar rikice-rikice.

Guterres ya bayyana haka ne yayin jawabi da ya yi a wajen taron tsaro na Munich karo da 53, inda ya nuna cewa, yanzu ana fuskantar kalubale a fannonin sauyin yanayi, karuwar yawan al'umma, matsalar karancin abinci da dai sauransu, wadanda da ke sanya kasashe yin gasa da juna wajen neman arziki, al'amarin dake kaiwa ga barkewar rikici a fadin duniya.

A ganin Guterres, samun ci gaba na iya karfafa karfin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, ta yadda zai kawar da barazanar barkewar rikici.

Guterres ya ce, ingantuwar tattalin arzikin duniya na taka muhimmiyar rawa wajen wadatar duniyar, sai dai wasu sassa ba sa kokarin bada ta su gudunmuwa yadda ya kamata.

Baya ga haka, Guterres ya yaba sosai da nasarorin da Sin ta samu wajen rage talauci. Inda ya ce, bai kamata a manta da ita ba, a matsayinta na wadda ta fi ba da tallafi wajen rage talauci a duniya cikin shekaru 10 da suka gabata. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China