in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 72 a kudancin Pakistan
2017-02-17 10:42:43 cri

An kai wani harin kunar bakin wake a wani wurin ibada dake da nisan kilomita 200 daga Karachi, fadar mulkin kasar Pakistan, yayin da mabiya addinin kusan 500 ko 800 suke yin addu'a. Shi dai wurin ibadar yana yankin Sehwan dake jihar Sindh ta kasar ta Pakistan. Kuma rahotanni dake fitowa daga gidan telebijin na kasar GEO na cewa, maharin ya kutsa ta cikin babbar kofar dakin ibadan ne, inda nan take ya tayar da bam din da ke jikinsa.

Wani wanda harin ya rutsa da shi kuma ya ke karba jinya ya shaida mana cewa, "Ina tsaya a kusa da dakin da aka sa na'urar sanya-ido a lokacin da harin ya auku, na ga jami'in da ke kula da wannan daki ya fita daga dakin, daga bisani kuma sai bam din ya tashi, ina tsammani, ko ya ga wani abu ne."

Wani mutum na daban wanda ya ganewa idonsa shi ma ya bayyana cewa, "Muna addu'a, sai kawai muka ji karar fashewar bam, daga baya sai muka ga gawawwaki warwatse ta ko ina."

Rundunar 'yan sandan yankin Sehwan ta bayyana cewa, a kalla mutane 72 ne harin ya rutsa da su, a cikinsu, akwai maza 43, mata kuwa 9, kana yara guda 20, ban da haka kuma kusan mutane 250 ne suka ji rauni a wurin, kila adadin mutanen da suka mutu zai karu saboda wasu sun ji munanan raunuka.

Kawo yanzu, an garzaya da wadanda suka ji rauni ta jiragen sama zuwa asibitocin yankunan dake kusa da yankin Sehwan domin a ba su kulawar da suke bukata, kana gwamnatin yankin ta bukaci rundunar sojojin kasar da su ba da taimakon da ake bukata.

Wani jami'in watsa labarai na rundunar sojojin kasar Pakistan ya bayyana cewa, babban hafsan hafsoshin sojojin kasa na kasar ya riga ya aika da sojoji zuwa wurin da harin ya auku domin tallafawa wadanda suka ji rauni

Kungiyar IS ta sanar da cewa, ita ce ta kai wannan hari ne a Pakistan.

Firayin ministan kasar ta Pakistan Nawaz Sharif ya yi Allah da wadai da babbar murya kan wannan harin, kuma ya bukaci masu aikin jinya na kasar da su gaggauta ceton wadanda suka ji rauni.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, an kai hare-hare da dama a kasar, a ranar 13 ga wata bisa agogon kasar, wani reshen kungiyar Taliban ta kasar ya kai harin kunar bakin wake a wani wurin da mutane suka taro a birnin Lahore, hedkwatar jihar Punjab ta kasar, inda mutane 15 suka rasa rayukansu, kana sama da 60 suka ji rauni, a ranar 15 ga wata, an sake kai wasu hare-haren kunar bakin wake har sau hudu a cikin yini guda, hare-haren da suka halaka mutane a kalla 6.

Bisa rahoton da cibiyar nazarin kwanciyar hankali ta kasar ta fitar, an ce, a bara, adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni a sanadiyar hare-haren ta'addanci a kasar ya ragu da kaso 45 bisa dari, wato 2610 kawai, amma a shekarar 2015, adadin ya kai 4647, duk da haka adadin mutanen da suka mutu sanadiyar harin ta'addanci a jihohin Balochistan da Punjab ya karu a bara. Cibiyar tana ganin cewa, adadin ya ragu a kasar, lamarin dake bayyana cewa, matakan da gwamnatin kasar ta dauka domin yaki da ta'addanci sun taka rawa matuka, musamamman ma a yankin arewacin Waziristan, amma duk da haka 'yan ta'adda da mayakan kungiyoyin masu tsattsauren ra'ayi suna kai hare-hare a wurare daban daban a fadin kasar ta Pakistan.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China