in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya yi shawarwari da Netanyahu
2017-02-16 10:49:59 cri

A jiya Laraba ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi shawarwari da Benjamin Netanyahu, firayin ministan kasar Isra'ila wanda ke yin ziyara a fadar Amurka ta "White House" dake birnin Washington. Yayin taron ganawa da manema labaran da suka shirya cikin hadin gwiwa kafin shawarwarin, shugaba Trump ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta goyi bayan duk shiri da zai kai ga kafa "kasashe biyu", ko "kasa guda daya", a kokarin tabbatar da zaman lafiya tsakanin sassan biyu wato Palestinu da Isra'ila za su amince da shi. Bayanai na nuna cewa, yanzu haka, gwamnatin Trump tana aiwatar da manufar goyon bayan Isra'ila, tare kuma da matsa lamba ga Iran, wannan wata alama ce dake nuna cewa, watakila manufar Amurka a yakin Gabas ta Tsakiya za ta sauya.

Kafin shugaba Trump ya fara mulki a kasar ta Amurka, ya tattauna da firayin minstan Isra'ila Netanyahu a shafin Twitter, a saboda haka, kasashen biyu wato Amurka da Isra'ila suna sa ran cewa, za su sake maido da huldar dake tsakanin su bayan shawarwarin da shugabannin biyu suka yi. Hakika, a yayin taron ganawa da manema labaran da sassan biyu suka shirya cikin hadin gwiwa, Trump da Netanyahu sun sake bayyana cewa, akwai huldar zumunta mai karfi a tsakanin Amurka da Isra'ila, kana sun bayyana matsaya guda da suka cimma a kan batun nukiliya na Iran, ban da haka, sun soki kudurin MDD game da shirin matsugunin Yahudawa na Isra'ila. Trump ya ce, zai yi kokari matuka domin ganin an cimma burin daddale wata yarjejeniyar da za ta kawo zaman lafiya tsakanin Palestinu da Isra'ila, amma wajibi ne sassan biyu su yi hangen nesa, Netanyahu shi ma ya amince da ra'ayin Trump. Trump yana mai cewa, "Ina la'akari ga shirin kafa 'kasashe biyu' ko shirin 'kasa guda daya', amma ko shakka babu zan goyi bayan duk wani shirin da sassan biyu za su amince da shi, ina kaunar wannan shirin, ni da kaina, ina maraba da dukkansu, amma gaskiya ina goyon bayan shirin da zai samu karbuwa daga wajen Netanyahu da Palestinawa da al'ummar dake zaune a matsugunin Yahudawan Isra'ila baki daya."

A cikin shekaru sama da goma da suka gabata, gwamnatin kasar Amurka tana aiwatar da manufar kafa kasashe biyu masu 'yancin gashin kai wato kasar Isra'ila da kasar Palestinu, hakan shi ma ka'ida ce da ta taba ba da jagoranci kan shawarwarin aka gudanar da Oslo da kuma taron Camp David. Kana shirin kafa "kasashe biyu" shi ma ya samu amincewar yawancin kasashen duniya, yanzu, sabon ra'ayin da Trump ya nuna ya bayyana cewa, kila manufar Amurka game da yankin Gabas ta Tsakiya za ta sauya.

A nasa bangare, firayin ministan Isra'ila Netanyahu ya bayyana cewa, yana bukatar wata yarjejeniyar shimfida zaman lafiya mai ma'ana. Ya ce, "Ba shi da wani amfani don aka kulla yarjejeniya maras ma'ana, shi ya sa na fi son a kulla yarjejeniya mai ma'ana da za ta yi tasiri, wajibi ne mu kara yin kokari domin bullo da wata sabuwar dabarar wanzar da zaman lafiya."

Tun bayan da Trump ya fara mulki a Amurka, Isra'ila ta zartas da dokar ba da iznin gina matsugunin a yammacin gabar kogin Jordan ba bisa ka'ida ba, kana ta yarda da gina sabbin gidajen kwana kusan dubu 6 a yankin, game da wannan, Amurka ba ta ce komai ba game da wannan batu, a yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya jiya, Trump ya bukaci Netanyahu da ya yi hakuri kawai. Trump yana mai cewa, "Ina fatan za ka yi hakuri game da batun matsugunan Yahudawa, za mu yi kokarin bullo da wata dabara domin daidaita batun, muna fatan za mu cimma wata yarjejeniya domin warware wannan matsalar, na hakikance cewa, za mu magance wannan matsala."

Game da batun canja matsugunin ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Kudus kuwa, Trump ya bayyana cewa, ya dace a yi haka, kuma ya jaddada cewa, yana mai da hankali kan batun sosai.

Duk da cewa, Trump ya bukaci sassan biyu wato Isra'ila da Palestinu da su kai zuciya nesa, alamu na nuna cewa, watakila zai goyi bayan Isra'ila, amma kawo yanzu, manufar gwamnatin Trump ba ta sauya ba a bayyane, wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar shi ma ya fayyace cewa, manufar kasar game da batun Palestinu da Isra'ila ba ta sauya ba tukuna. Kwararren dake nazarin manufofin Amurka kan Gabas ta kusa wato yankin dake arewa maso gabashin Afirka da yankin dake kudu maso yammacin Asiya David Makovsky yana ganin cewa, ziyarar da Netanyahu ke yi a Amurka tana da ma'ana matuka, saboda a halin da ake ciki yanzu, ba a tabbatar da manufar kasar kan yankin Gabas ta Tsakiya ba, don haka, ziyarar wata dama ce ga shugaban Isra'ila, ta yadda zai yi tasiri ga gwamnatin Amurka kafin ta tsara manufar da abin ya shafa. Haka kuma ziyarar za ta taka rawa wajen karfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba ta hanyar yin musanyar ra'ayoyi kan wasu manyan batutuwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China