in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon sakataren tsaron Amurka zai halarci taron ministocin tsaron NATO
2017-02-15 10:32:49 cri

Za a gudanar da taron ministocin tsaron kasashen da suka sanya hannu a kan yarjejeniyar tsaron tekun arewacin Atlantic wato NATO tsakanin ranakun 15 da 16 ga wata, kuma wannan shi ne karo na farko da sabon sakataren tsaron kasar Amurka James Mattis zai halarci taron a madadin gwamnatin kasarsa. Kafin wannan, shugaban Amurka Donald Trump ya taba sukar kungiyar, inda ya yi zargi cewa, wasu kasashen wakilan kungiyar ba su biya kudin karo karo game da tsaro da aka saba biya ba, a sanadin haka, wasu kasashen Turai sun nuna damuwa kan lamarin, to, wane irin batu ake sa ran za a tattauna yayin taron ministocin tsaron NATO? Wadanne matakai kasashe wakilan kungiyar za su dauka game da zargin da gwamnatin Trump ta yi?

Kamar yadda aka saba, babban sakataren kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya shirya wani taron ganawa da manema labarai a jiya Litinin kafin gudanar da taron ministocin tsaron kungiyar, inda ya bayyana cewa, kudin karo karo na tsaro ba shi kadai da za a tattauna a yayin taron ministocin tsaron ba, amma yana daga cikin muhimmin batu da za a tattauna yayin taron kolin kungiyar da za a gudanar a watan Mayu mai zuwa. Yana mai cewa, "Dalilin da ya sa na fadi haka shi ne hakkin daukacin kasashen wakilan kungiyar NATO 28 su samar da tsaro ga al'ummomin fadin duniya, idan yanayin tsaro ya kyautata, to, za a iya rage adadin kudin karo karo da ake biya, idan kuma lamarin ya kara tsananta, to, dole ne a kara yawan kudaden da ake biya."

Tun bayan da aka kammala yakin cacar baka, wasu kasashen wakilan kungiyar NATO kamar kasashen Turai da Canada suka rage kudin karo karo da suke biya, amma yanzu yanayin ya sauya, a saboda haka shugabannin kasashen wakilan NATO sun cimma matsaya daya a taron kolin da suka gudanar a Wales na Birtaniya a shekarar 2014, inda suka yi alkawari cewa, za su kara biyan kudin karo karo kan jami'an tsaro a cikin shekaru goma masu zuwa, inda adadin kudin da za su biya zai kai kaso 2 bisa dari na adadin GDP nasu. Amma kawo yanzu, kasashe biyar wato Amurka da Birtaniya da Estonia da Poland da kuma Girka ne kawai suka cika alkawarinsu. Bayan da Trump ya fara mulki a Amurka, wasu kasashe wakilan NATO suna cikin zulumin cewa, kila gwamnatin Trump za ta bukaci sauran kasashe da su cika wannan alkawari kafin lokaci.

A ranar 6 ga wata, yayin da yake rangadin aiki a sansanin sojojin sama na MacDill dake lardin Florida na kasar, Trump ya sake jaddada cewa, Amurka tana goyon bayan NATO, amma ya kara da cewa, wajibi ne kasashen wakilan NATO su biya kudin karo karo cikin lokaci. Trump yana mai cewa, "Muna goyon bayan NATO, muna fatan daukacin kasashen wakilan kungiyar za su biya kudin karo karo cikin lokaci kuma yadda ya kamata, yanzu kasashe da dama ba su biya ba tukuna, wasu kuma ba su biya isasshen kudin da ya kamata su biya ba."

Yayin taron manema labaran, Stoltenberg shi ma ya yarda cewa, NATO tana fuskantar matsin lamba daga wajen Trump kan batun biya kudin karo karo domin samar da tsaro, shi kansa ya amince da ra'ayin Trump. Ya ce, "Ni da shugaban Amurka Trump mun taba tattaunawa kan batun biyan kudin samar da tsaro sau biyu ta wayar tarho, inda ya sha bayyanawa cewa, yana goyon bayan NATO, kana ya jaddada muhimmancin adalci wajen biyan kudin karo karo domin samar da tsaro, ya kuma nuna cewa, kasashen da ba su biya kudin karo karo game da jami'an tsaro da adadinsa ya kai kaso 2 bisa na GDP nasu ba, dole ne su kara biya. Gaskiya na amince da ra'ayinsa."

Stoltenberg ya sanar da cewa, NATO ta samu kyautatuwa a fannin karbar kudin karo karo ta fannin samar da tsaro, alkaluman da aka fitar a shekarar 2016, na nuna cewa, adadin kudin da aka kashe wajen samar da tsaro a kasashe wakilan kungiyar NATO dake Turai da kasar Canada ya karu da kaso 3.8 bisa dari, adadin da ya dara hasashen da aka yi, ana iya cewa, adadin kudin da NATO ta kashe a fannin samar da tsaro a bara ya karu har kusan dalar Amurka biliyan 10.

Kazalika, game da ra'ayin da gwamnatin Amurka za ta dauka kan NATO, Stoltenberg ya bayyana cewa, sakataren tsaron Amurka Mattis zai halarci taron ministocin NATO, an sa ran za su tattaunawa da shi a yayin taron, musamman ma game da yadda za a kara daukan matakan yaki da ayyukan ta'addanci. Stoltenberg ya jaddada cewa, shugaban Amurka da sakataren harkokin wajen kasar da sakataren tsaron kasar dukkansu sun bayyana ta wayar tarho cewa, Amurka tana goyon bayan NATO.

Game da huldar dake tsakanin Amurka da Rasha kuwa, Stoltenberg ya ce, Amurka tana goyon bayan manufar NATO kan Rasha wato yaki da kuma tattaunawa, shi ya sa NATO ta yi maraba da shawarwarin dake tsakanin Amurka da Rasha.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China