in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da kyautata zuba jari a ketare a shekarar 2017
2017-02-10 10:13:52 cri

Jiya Alhamis kakakin watsa labarai na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Sun Jiwen, ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, a shekarar 2017 da ake ciki, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da kyautata zuba jari kai tsaye a kasashen ketare, kana tana fatan kasashen duniya za su yi kokari tare, domin yaki da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, tare kuma da sa kaimi ga zuba jari ba tare da rufa rufa ba a fadin duniya. Ban da haka, Sun Jiwen ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ingiza gudanarwar shirin "ziri daya da hanya daya", domin kara samun sakamakon da zai haifar da moriya ga kasashen da abin ya shafa.

Bisa alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar, an ce a shekarar 2016 da ta gabata, gaba daya adadin jarin da ba na hada hadar kudi ba da kasar Sin ta zuba a kasashen ketare, ya kai dalar Amurka biliyan 170 da miliyan 110, adadin da ya karu da kaso 44.1 bisa dari, idan aka kwatanta shi da na shekarar 2015, wanda a yanzu ya ninki har sau 3.

Kana jimillar jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen ketare, da adadin da ta zuba a nahiyoyin Amurka da Turai da kuma Australia, sun kai matsayin koli a tarihi.

Sai dai a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, kuma wasu kasashe suna ba da kariya ga cinikayya da kuma zuba jari, har ta kai wasu kasashen na gyara manufofin zuba jari da suke aiwatarwa ga 'yan kasuwa na kasashen ketare. Kakakin watsa labarai na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Sun Jiwen ya bayyana cewa, "Yanzu haka kasuwar hada hadar kudin kasashen duniya tana da tangarda, kuma wasu kasashe ba su da tabbaci kan manufofin tattalin arzikinsu, kana wasu kasashe masu ci gaba, suna kayyaden zuba jarin da kasar Sin ke yi, musamman ma ga kamfanonin gwamnatin kasar Sin, hakan ya haifar da hadari da rashin tabbas ga kamfanonin kasar Sin, yayin da suke zuba jari a ketare."

Game da yanayin zuba jari a ketare da kasar Sin ke ciki a shekarar 2017, Sun Jiwen ya bayyana cewa, yanayin zai kyautata sannu a hankali, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kamfanonin kasar domin su kara zuba jari a ketare bisa ka'ida, tare kuma da magance hadarin da suke fuskanta, kana ya kara da cewa, kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su yi kokari tare, domin yaki da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, ta yadda za a sa kaimi kan zuba jari ba tare da rufa rufa ba a fadin duniya. Sun Jiwen yana mai cewa, "Muna fatan kasashen duniya za su gama kai domin yaki da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, tare kuma da sa kaimi kan zuba jari ba tare da rufa rufa ba a fadin duniya, ta haka ne za a kai ga kafa wani tsarin yin hadin gwiwa domin moriyar juna, wanda zai taimaka wajen samun wadata tare."

Tun bayan da aka bullo da shirin "ziri daya da hanya daya", shirin ya jawo hankalin jama'a, kuma yanzu ana gudanar da ayyuka daban daban karkashin shirin lami lafiya, amma wasu hukumomi suna ganin cewa, kila ne akwai wuya a samu riba daga wajen su. Sun Jiwen ya ce, "Gaskiya wasu ayyukan dake shafar shirin 'ziri daya da hanya daya', musamman ma ayyukan samar da kayayyakin more rayuwar jama'a, za su bukaci kashe kudi da dama, kuma za su dauki lokaci mai yawa. Ga alama, mawuyaci ne a samu riba daga gare su, ko da yake ya zama wajibi mu yi hangen nesa, duba da cewa wadannan ayyukan za su kyautata rayuwar al'ummomin kasashen da shirin ya shafa, don haka ana iya cewa, suna da babbar ma'ana. Nan gaba kuma, za su kara sa kaimi ga cin nasarar shirin, tare kuma da kara zurfafa hadin gwiwar zuba jari dake tsakanin kasar Sin da kasashen da shirin ya shafa. Ana sa ran za a samu riba daga gare su."

Kwanakin baya ba da dadewa ba, babban taron masana'antu da kasuwancin kasar Jamus, ya fitar da jerin sunayen kasashen dake gudanar da cinikayya da kasar a shekarar 2016. A karo na farko, kasar Sin ta kai sahun gaba a cikin shirin, inda ta kasance abokiyar cinikayya ta farko ta kasar ta Jamus. Game da wannan, Sun Jiwen ya bayyana cewa, a shekarar 2016, adadin cinikayya dake tsakanin Sin da Jamus ya kai dalar Amurka biliyan 151 da miliyan 290, duk da cewa, adadin ya ragu da kaso 3.5 bisa dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2015, a hannu gudu adadin zuba jari tsakanin sassan biyu ya karu cikin sauri. Ya zuwa karshen shekarar bara, adadin jarin da Jamus ta zuba a kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 8 da miliyan 180, kana adadin jari, da ba na hada hadar kudi ba, wanda kasar Sin ta zuba a Jamus ya kai dalar Amurka biliyan 8 da miliyan 830. Sun Jiwen ya yi hasashe kan makomar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Jamus, inda ya bayyana cewa, "Zuwa shekarar 2017, an cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Jamus, kuma manyan jami'an sassan biyu za su ci gaba da kai wa juna ziyara, kana hadin gwiwa dake tsakaninsu a fannonin cinikayya, da zuba jari, da kasuwanni, da kirar na'urorin zamani, na da makoma mai haske. Haka kuma hulda tsakanin sassan biyu za ta taimaka matuka, wajen fadada huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da kasashen Turai." (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China