in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin manoman Sin da za su yi sabbin sana'o'i zai zarta miliyan 20 nan zuwa 2020
2017-02-08 10:09:24 cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, majalissar gudanarwa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta fitar da takarda ta farko a shekarar nan ta 2017, inda aka gabatar da sabbin manufofin gwamnatin kasar ta Sin, na fannonin sa kaimi kan kwaskwarimar aikin gona, da hanzarta ci gaban kauyuka, tare kuma da kara kudin shiga na manoma.

Ana dai iya cewa, wannan takarda ta samar da sabbin damammaki ga manoman kasar Sin, wadanda ke kokarin neman samun ci gaba ta hanyar gudanar da sabbin sana'o'i.

Kawo yanzu, Zhao Wenguang wanda ya taba kasancewa malamin makarantar midil a yankin Tongzhou na birnin Beijing, ya riga ya shiga shekara ta goma yana shuka 'ya'yan itatuwa, kuma yana ganin cewa, aikin gona irin na zamani yana da babban fiffiko, kuma yana da makoma mai haske. Zhao Wenguang ya bayyana cewa, "Wani abokina yana shuka wake a yankin arewa maso gabashin kasar Sin, waken da yake shukawa irin na gargajiya ne, ba irin wanda aka sauya kwayoyin hallitar sa kamar yadda ake yi a kasashen waje ba ne, kuma waken da abokina ya shuka ya fi inganci. Duk da cewa, yana bukatar karin lokaci, ina ganin cewa, yanzu haka a kasar Sin, aikin gona yana da makoma mai haske."

A halin da ake ciki yanzu, manoma kamar Zhao Wenguang wadanda suka kware wajen fasaha da kasuwanci suna karuwa cikin sauri, dalilin da ya sa haka shi ne domin gwamnatin kasar Sin ta samar da goyon baya wajen tsara manufofi, kuma ta samar da horo ga manoman kasar.

Kwararre kan batun aikin gona kuma shehun malamin dake aiki a cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'umma ta kasar Sin Li Guoxiang ya dauka cewa, sabbin sana'o'in aikin gonar da manoman kasar ke gudanarwa, za su taimaka wajen cimma burin tabbatar da dauwamammen ci gaban aikin gona, da raya kauyuka a kasar Sin, su ma za su warware matsalolin karancin manoma da ake fuskanta. Li Guoxiang yana bayyana cewa, "Yanzu yawancin manoman kasar Sin suna shiga manyan garuruwa, kuma suna gudanar da ayyuka da ba na aikin gona ba. A kauyuka da dama tsoffi da mata ne kadai ke zama, a saboda haka babu wadnda za su shuka hatsi a gonaki, idan ana son warware wannan matsala, wajibi ne a horas da manoma wadanda za su iya gudanar da sabbin sana'o'i. Ga misali a horas da samari wadanda za su kware wajen fasaha da kuma kasuwanci."

Yanzu haka an fitar da takardar farko ta majalissar gudanarwa, ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a hukumance, wadda ta bayyana cewa, za a ci gaba da horas da manoma domin su gudanar da sabbin sana'o'in aikin gona, musamman ma za a kara mai da hankali kan manoman da za su koma kauyuka daga garuruwa, ta yadda adadin manoman da za a horas da su zai kai miliyan 1.

Takardar dai ta jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara karfafa kwaskwarima kan tsarin aikin gona, domin sa kaimi kan ci gabansa, Li Guoxiang yana ganin cewa, kwaskwarimar tana shafar fannoni daban daban na ci gaban aikin gona, da gine-ginen kauyuka a kasar Sin. Haka kuma za ta kara jawo hankalin manoma su koma kauyuka, domin gudanar da sabbin sana'o'in aikin gona. Li Guoxiang ya ce, "Daga takardar farko da aka fitar, ana iya gano cewa, gwamnatin kasar Sin ta samar da sharruda masu inganci ga manoma, ana sa ran cewa, shirin horon da ake samarwa manoma zai samu sakamako mai faranta ran mutane."

Ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ita ma ta fitar da shirin horas da manoma, domin su gudanar da sabbin sana'o'i a lokacin da ake gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13, inda ta bayyana cewa, za a horas da manoma wadanda za su gudanar da sabbin sana'o'in aikin gona sama da miliyan 20 nan zuwa shekarar 2020, ko shakka babu shirin zai taimaka matuka wajen ci gaban aikin gona a kasar Sin. Game da wannan, Li Guoxiang yana ganin cewa, idan ana son cimma wannan buri, ana bukatar dogon lokaci, kuma ana bukatar goyon bayan manufofin gwamnati, ta hakan manoman za su more wannan manufa. Mr. Li Guoxiang ya ce, "Gwamnatin kasa za ta kara samar da gatanci ga manoma, musamman ma wajen tsara manufofi da kudi. Idan yanayin zaman rayuwa a kauyuka ya kyautata, manoma ba za su rika fita zuwa birane ba, kuma za su gudanar da sabbin sana'o'i irin na zamani a kauyuka. Da haka kuma aikin gona zai samu ci gaba yadda ya kamata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China