in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata Amurka ta tsokaci cikin batun tekun kudancin kasar Sin ba
2017-02-07 11:16:52 cri
Kwanan baya, a yayin da yake ziyarar aiki a kasar Japan, ministan harkokin tsaron kasar Amurka James Mattis, ya bayyana cewa, ba a bukatar yin sauye-sauye a harkar aikin soji a yankin tekun kudancin kasar Sin a halin yanzu, yana mai cewa, matakin da kasar Sin ta dauka a yankin, ya lalata yanayin fahimtar juna dake tsakanin kasashen yankin.

Dangane da wannan lamari, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen da batun ya shafa su warware matsalar tekun kudancin kasar Sin ta hanyar siyasa kai tsaye, sabo da hakan ne kawai zai dace da moriyar dukkan kasashen dake yankin, kuma ana fatan kasashen da ba sa cikin yankin za su mutunta fata, da kuma moriyar kasashen dake yankin tekun kudancin kasar Sin.

Haka kuma, Lu Kang ya ce, ko shakka babu, ba bukatar kasar Amurka ta dauki matakan soja a yankin tekun kudancin kasar Sin, sabo da ba ta yankin, sa'an nan ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan kasashen da abin ya shafa za su iya warware matsalar su ta hanyar siyasa, tare da warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar gudanar da shawarwari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China