in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kakabawa Iran sabon takunkumi
2017-02-06 10:54:08 cri

Kwanan baya, ma'aikatar kudin Amurka ta sanyawa wadansu daidaikun mutane takunkumi, wadanda ke tallafawa kungiyar Quds Force dake karkashin dakarun juyin-juya-hali na Iran wato IRGC, kana da nuna goyon-baya ga shirin da Iran ke aiwatarwa, na harba makamai masu linzami, a wani yunkuri na mayar da martani ga gwajin da Iran ta yi na harba makamai masu linzami a kwanan baya, gami da 'goyon-bayan ayyukan ta'addanci'.

Manazarta sun ce, ko da yake sabon takunkumin ba zai yi babban tasiri ga kasar Iran ba, amma hakan zai bude sabon shafi na takun-saka tsakanin Amurka da Iran.

Kwanan baya, kasar Iran ta yi wani gwaji na harba makamai masu linzami, al'amarin da ya janyo sabon takunkumin da Amurka ta sanyawa Iran. Bayan aukuwar lamarin, manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu sun fara wani ce-ce-ku-ce, inda mai taimakawa shugaban Amurka kan harkokin tsaro Michael Flynn ya gargadi Iran da cewa, ayyukan da ta yi sun kawo illa ga kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, kana sun kawo babbar barazana ga kasashe aminan Amurka.

Yayin da Barack Obama ke rike da ragamar mulkin Amurka, gwamnatinsa ta taba kakabawa Iran irin wannan takunkumi, amma yawancin mutanen da Amurkar ta sanyawa takunkumin 'yan Iran ne, gami da jami'an soja dake da nasaba da harkar harba makamai masu linzami, a rundunar dakarun IRGC. Sai dai takunkumin da aka sanyawa Iran a wannan karo, ya shafi karin mutane daga kasashe da dama.

A ranar da Amurka ta sanar da a kakabawa Iran takunkumin, shugaban kasar Donald Trump shi ma ya sake gargadin Iran. Lokacin da yake yakin neman zabe, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba Trump ya yi kakkausar suka game da yarjejeniyar da aka cimma kan batun nukiliyar Iran, inda ya bukaci da a soke wannan yarjejeniya gami da sake gudanar da shawarwari.

Amma a baya bayan nan, sabon ministan tsaron Amurka gami da sakataren harkokin wajen kasar, sun bayyana cewa, a cikin akalla shekaru 10, aiwatar da yarjejeniyar nukiliya ta Iran zai iya takawa Iran birki a fannin gudanar da gwajin makaman nukiliya, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki. Haka kuma a halin yanzu, babu shaidun dake nuna cewa, a cikin wani kankanin lokaci, Trump zai dauki mataki kan yarjejeniyar.

Sai dai wannan sabon takunkumi ya janyo babban martani daga kasar ta Iran. Iran na ganin cewa, zargin da Amurka ta yi, ba shi da tushe ko kadan balle makama. Takunkumin da Amurka ta sanyawa Iran ba ma kawai ya sabawa ka'idojin yarjejeniyar nukiliya na Iran ba, har ma ya sabawa alkawarin da Amurka ta dauka dake cewar, ba za ta yi katsalandan cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe ba.

A cewar Iran, makasudin yin gwajin makamai masu linzami shi ne tsaron gida kawai, kana kuma Iran ba za ta yi amfani da shi ta sauran wasu fannoni ba, hakan bai sabawa yarjejeniyar nukiliyar Iran ba. Iran ba ta tsoron duk wata bazarana daga ketare, kuma za ta ci gaba da daukar matakan kare kanta ta fuskar soja, ciki har da yin nazari kan makamai masu linzami.

Har wa yau kuma, Iran ta jaddada cewa, takunkumin da Amurka ta sanya mata, wauta ce da kuma rashin nazari, kuma ba zai hana ta tsayawa ga aiwatar da manufofinta na wanzar da zaman lafiya, da yaki da ta'addanci gami da yaki da masu tsattsauran ra'ayi ba. Iran ta ci gaba da cewa, domin yin ramuwar gayya kan Amurka, za ta dakatar da bayar da takardar biza ga 'yan Amurka, da sanyawa wasu daidaikun Amurkawa dake tallafawa kungiyoyin 'yan ta'adda takunkumi ta fuskar doka.

A nasa bangaren, yayin da yake yakin neman zaben shugabancin Amurka, Donald Trump bai taba amincewa da yarjejeniyar nukiliya ta Iran ba, al'amarin da ya sa bangarori daban-daban na Iran suka damu sosai kan makomar dangantakar Iran da Amurka. Haka kuma wasu kwararan matakan da gwamnatin Trump ta dauka a kwanan baya, sun kara irin wannan damuwa, ciki har da haramtawa Iraniyawa, da na sauran wasu kasashe shiga cikin Amurkar.

Kafofin watsa labaran Amurka sun ce, a lokacin gwamnatin Obama, Amurka tana son cimma matsaya daya tare da Iran kan yarjejeniyar nukiliya, da kulla dangantakar hadin-gwiwa ta fannin yaki da ta'addaci, ta yadda alakar kasashen biyu za ta bunkasa yadda ya kamata. Amma ba'a cimma wannan kyakkyawan buri ba har yanzu.

Masu bada sharhi na yau da kullum na Amurka sun nuna cewa, ko da yake sabon takunkumin da Amurka ta sanyawa Iran ba lalle ne ya yi wani cikakken tasiri ba, amma duk da haka zai kara haddasa zaman doya da manja tsakanin kasashen biyu, kuma akwai rashin tabbas game da sakamakon da takunkumin zai haifar. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China