in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da kasashen Afirka suna kara karfafa hadin gwiwa domin cimma burin muradun AU nan da shekarar 2063
2017-02-03 10:42:32 cri

A kwanakin baya ne, aka rufe taron kolin kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU karo na 28 a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda aka tattauna game da yadda za a cimma burin tabbatar da muradun kungiyar nan da shekarar 2063 ta hanyar zuba jari a bangaren matasa.

Kwararru a fannin ci gaban kasashen Afirka suna ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashen Afirka suna fuskantar kalubale a fannoni daban daban yayin da suke kokarin neman samun dauwamammen ci gaba bisa dogaro kansu, kana manufar shirin "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar da manufar muradun AU nan da shekarar 2063 kusan iri guda ne, a saboda haka, idan sassan biyu wato Sin da kasashen Afirka suka kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu, to, matakan za su taimakawa kokarin da ake domin cimma burin muradun yadda ya kamata.

AU ta zartas da muradunta game da neman samun dauwamammen ci gaban kasashen Afirka nan da shekarar 2063 ne a shekarar 2015, makasudin tsara wannan muradun shi ne domin kafa sabuwar nahiyar Afirka mai wadata a cikin shekaru 50 masu zuwa. Yayin taron kolin da aka gudanar a birnin Addis Ababa, mahalarta taron sun tattauna game da yadda za a cimma wannan burin ta hanyar zuba jari a bangaren matasa.

A jawabinta yayin bikin bude taron kolin, tsohuwar shugabar hukumar zartarwar kungiyar AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta yi nuni da cewa, gaba daya akwai matasa wadanda shekarun haihuwarsu suka kai 15 zuwa 24 sama da miliyan 200 a fadin Afirka, ko shakka babu za su taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban nahiyar, saboda haka wajibi ne a kara zuba jari a bangaren matasan domin samar musu damammaki. Madam, Zuma ta jaddada cewa, matasa da dama a nahiyar suna fama da matsalar rasa aikin yi, idan ana son a magance wannan matsalar, wajibi ne a kara karfafa aikin samar musu da ilimi, da kuma horo.

Nkosazana Dlamini-Zuma ta sanar da cewa, bana kungiyar AU za ta nada wani manzon musamman mai kula da harkokin matasa domin samar da taimako ga matasan Afirka a fannin samun aikin yi.

Mamba mai kula da harkokin kwadago da kimiyya da fasaha na AU ya gaya wa wakilin Xinhua na kasar Sin cewa, kamata ya yi gwamnatocin kasashen Afirka su kara zuba jari a bangaren da ya shafi matasa, hakan ba ma kawai zai horas da su yadda ya kamata ba, har ma zai hana kwararru matasa su tafi ketare domin neman aikin yi, wannan zai taimakawa kasashen Afirka su iya samun ci gaba bisa dogaro da kansu. Ya kuma fayyace cewa, kungiyar AU tana shirin bullo da wasu shirye-shirye domin samar da goyon baya ga matasa.

Duk da cewa, muradun AU nan da shekarar 2063 zai taimaka matuka ga ci gaban Afirka, amma kwararrun da abin ya shafa suna ganin cewa, kasashen Afirka suna fama da kalubale mai tsanani bisa dalilai da dama.

Darektar sashen Afirka ta asusun ba da lamuni na duniya wato IMF Antoinette Sayakh tana ganin cewa, ko da yake kasashen Afirka sun samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri a cikin shekaru 15 da suka gabata, kuma al'ummomin kasashen sun samu kyautatuwa a fannin kiwon lafiya da zaman rayuwa, amma har yanzu suna cikin mawuyacin hali. Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, ya zuwa shekarar 2015, saurin karuwar tattalin arzikin Afirka ya ragu, inda ya yi kasa sosai a cikin shekaru 15 da suka gabata, ban da haka kuma, an yi hasashen cewa, a shekarar 2016 da ta gabata, saurin karuwar tattalin arzikin nahiyar ya kara raguwa.

Madam Dlamini-Zuma ta taba bayyana cewa, bayan da Donald Trump ya hau kan kujerar shugabancin kasar Amurka, kungiyar AU ta shiga wani lokaci mai sarkakiya, sakamakon sabon umurnin da ya bayar game da hana wasu mutane shiga kasarsa wanda ya yi babban tasiri ga kasashen Afirka.

A saboda haka, Dlamini-Zuma ta bayyana cewa, idan kasashen Afirka suna son kara samun bunkasuwa, kamata ya yi su kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu da sauran kasashen duniya, musamman ma da kasar Sin.

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya taba bayyana cewa, shirin "ziri daya da hanya daya" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yana da manufar samun wadata tare, kasar Sin tana maraba da kasashen Afirka domin su shiga shirin.

Yanzu dai, shirin "ziri daya da hanya daya" na kasar Sin yana taimakawa matuka wajen samar da kayayyakin more rayuwar jama'a a kasashen Afirka, haka nan shirin ya samar da guraben aikin yi da dama ga matasan nahiyar, ana iya cewa, kokarin da kasar Sin take ya samu yabo matuka daga wajen kasashen Afirka, kana zai taimaka wajen tabbatar da muradun AU nan da shekarar 2063.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China