in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar Sin da Afirka ta taimaka ga ci gaban nahiyar, in ji Amina
2017-01-27 12:52:57 cri
Ministar harkokin wajen kasar Kenya Amina Mohammd ta bayyana a jiya Alhamis cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ta taimaka matuka ga samun ci gaban nahiyar da kowa ke iya gani a zahiri bisa tushen cin moriyar juna.

Ministar wadda ta bayyana hakan yayin wata zantawa da manema labarai a gefen taron kolin kungiyar tarayyar Afirka da ke gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha, ta kuma bayyana cewa, dangantakar sassan biyu ta kara taimakawa nahiyar wajen magance matsalolin da suka dade suna damunta.

Ta kuma lura da cewa, an cimma nasarori da dama tun bayan taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) wanda aka gudanar a shekarar 2015 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, inda kasar Sin ta sanar da samarwa nahiyar dala biliyan 60 a matsayin rance da tallafin raya kasashen na Afirka, baya ga guraben ayyukan yi da kamfanonin kasar Sin da ke aiki a nahiyar suka samar.

Ta ce a Kenya kadai,kasar Sin ta dauki nauyin gina layin dogo da ya hade tashar jiragen ruwa mafi girma a yankin gabashin Afirka ta Mombasa zuwa birnin Nairobi, fadar mulkin kasar ta Kenya, layin da ake fatan gwada shi a watan Yunin wannan shekara. Ana kuma fatan zai taimakaa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. Aikin wanda kamfanin kasar Sin ya ke gudanarwa, ya kuma samar da dubban guraben ayyukan yi ga al'ummomin yankin.

Ministar ta ce, kayayyakin more rayuwa su ne abubuwan da kasashen Afirka suke bukata don bunkasa masana'antunsu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China