in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu iyalai Sinawa na kara haihuwar yara zuwa biyu
2017-01-24 12:28:08 cri

Kwanakin baya, kwamitin kula da kiwon lafiya da shirin haihuwa na kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar 2016 da ta gabata, adadin jariran da aka haifa a kasar ta Sin, ya zarta miliyan 17 da dubu 860, adadin da ya karu sama da na sauran shekaru tun bayan shekarar 2000, an ce cikin jariran da aka haifa, adadin jarirai na biyu ga mahaifan su, ya karu bisa babban mataki.

Shugaban hukumar ba da jagoranci kan aikin shirin haihuwa ta kwamitin kula da kiwon lafiya da shirin haihuwa na kasar Sin Yang Wenzhuang, ya bayyana cewa, kafin shekarar 2013, adadin jarirai na biyu ga mahaifan su cikin iyalai Sinawa da aka haifi, bai wuce kaso 30 bisa dari kacal ba, amma ya zuwa shekarar 2016, adadin ya karu zuwa kaso 45 bisa dari.

Yang Wenzhuang ya kara da cewa, bara wato shekara ta 2016, shekara ta uku ke nan da aka fara aiwatar da manufar haihuwar jarirai na biyu a cikin iyali guda, wanda miji ko mata ya fito ne daga iyalan da suka haifi jariri daya kacal. Kana ita ce shekara ta farko da aka fara aiwatar da manufar haihuwar jairirai guda biyu a cikin kowanen iyali a fadin kasar Sin.

Ana iya cewa, sannu a hankali ana samun sakamako a wannan fanni. Wato adadin jariran da aka haife su bisa amincewar manufar da gwamnatin kasar Sin ta tsara ya karu a bayyane. Yang Wenzhuang ya ce, "Bisa binciken da hukumar kididdigar kasar Sin ta yi, an ce, adadin jariran da aka haife su a bara ya kai miliyan 17 da dubu 860, Kana bisa alkaluman da aka samar, an ce, adadin jarirai da aka haife su a cikin asibitoci a duk shekarar bara ya kai miliyan 18 da dubu 460, lamarin da ya shaida cewa, al'ummar kasar Sin na goyon bayan sabuwar manufar da gwamnatin kasar ke aiwatarwa a fannin shirin haihuwa. Misali, a shekarar 2000, adadin jariran da aka haife su a kasar Sin, ya kai miliyan 17 da dubu 710, daga baya wato ya zuwa shekarar 2002, adadin ya ragu zuwa miliyan 16 da dubu 470 kacal. Kana tsakanin shekarar 2003 da ta 2013, adadin ya kai wajen miliyan 16.

A kuma shekarar 2014, gwamnatin kasar Sin ta fara yin kokarin kyautata manufar shirin haihuwa, wanda a bayyane adadin ya karu, musamman ma a shekarar 2016, adadin ya zarta miliyan 17 da dubu 860. Wanda ya kasance mafi yawa tun bayan shekarar 2000. A saboda haka ana iya cewa, sabuwar manufar ta samu sakamako a bayyane."

Duk da cewa, an samu sakamako a fannin, amma a wasu birane, musamman ma a nan birnin Beijing, da kyar wasu masu juna biyu ke shiga asibiti domin haihuwa. Game da wannan batu, shugaban hukumar kula da mata da yara ta kwamitin kula da kiwon lafiya, da shirin haihuwa na kasar Sin Qin Geng ya bayyana cewa, "A cikin shirin da aka tsara kan aikin kiwon lafiya yayin da ake gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13 a nan kasar Sin, an tanadi cewa, za a kara samar da gadaje ga masu juna biyu, wadanda za su kai dubu 89 a fadin kasar. Kana za a kara kyautata tsarin samar da hidima ga mata da yara cikin gajeren lokaci. Ban da haka kuma, za a kara kokari matuka, domin kara gina cibiyoyin kula da masu juna biyu, da jarirai, wadanda ke cikin hadari. Kazalika, za a kara horas da likitocin da abin ya shafa, yadda adadinsu zai kai dubu 140. Ana sa ran cewa, za a kara kyautata aikin ba da hidima ga masu juna biyu, da jararai yadda ya kamata."

Shugaban hukumar ba da jagoranci kan aikin shirin haihuwa, ta kwamitin kula da kiwon lafiya, da shirin haihuwa na kasar Sin Yang Wenzhuang ya ce, bisa bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar Sin, ingancin zaman rayuwar al'ummar kasar ya kara kyatatuwa. A karkashin irin wannan hali, tabbas ana bukarar karin kudade yayin da ake renon yara, wanda zai yi tasiri ga haihuwa lafiya. Yang Wenzhuang yana mai cewa, "Bisa alkaluman da aka fitar a shekarar 2015, an ce, adadin mutanen da ba su son su haifi jariri na biyu a cikin iyalinsu, bisa dalilin kudi ya kai kaso 74.5 bisa dari, kana adadin mutanen da ba su son su haifi jariri na biyu a cikin iyalinsu bisa dalilin karancin lokacin kula da yara, ya kai kaso 61.1 bisa dari. Don haka tabbas ana fuskantar matsaloli da dama yayin da ake tunanin kara haihuwa."

Yang Wenzhuang ya ci gaba da cewa, sassan da abin ya shafa sama da 40 na majalisar gudanarwar kasar Sin, suna sanya kokari matuka domin tsara manufofin kyautata sharruda a fannoni daban daban. Miisali fannin kiwon lafiya, da renon yara, da ba da ilmi, da inshura, da haraji da sauransu ga al'ummar kasar Sin, ta yadda za su tsai da kudurin haifi jariri na biyu a cikin iyali guda.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China