in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun Sin suna taimakawa Burundi wajen noman shinkafa
2017-01-23 13:22:39 cri

Burundi kasa ce dake nahiyar Afirka, wadda ke fama da talauci mai tsakani, kana tattalin arzikinta yana dogaro ne kan aikin gona, amma shinkafar da manoman kasar suke nomawa ba ta da inganci, a saboda haka al'ummar kasar ke fama da matsalar karancin abinci mai tsanani.

Domin samar da taimakon fasaha gare ta, kasar Sin ta tura tawagogin kwararrun aikin gona har sau uku, inda ya zuwa shekarar 2016, kwararrun suka cima babban sakamako da ya zamo a sahun gaba a fadin nahiyar Afirka, wajen samun hatsi a ko wace hekta a duk tsawon shekara.

Yawancin kwararru a fannin noma da gwamnatin kasar Sin ta tura ga kasar ta Burundi, bisa matakai uku, sun fito ne daga lardin Sichuan, wanda ke da fiffiko wajen aikin gona a fadin kasar Sin, wadannan kwararrun sun kware ne a fannonin shuka shinkafa, da kiwon dabbobi, da kiwon dabbobin ruwa, da nazarin gonaki da taki, da kiwon lafiyar dabbobi, da injunan aikin gona. Kwararrun sun sauka a kasar Burundi ne a watan Nuwamban shekarar 2015, nan take kuma suka nuna kwazo da himma kan aikinsu.

Domin kara kyautata ingancin shinkafa a kasar ta Burundi, kwararrun kasar Sin sun yi nazari sosai kan hakikanin sharuddan halittun kasar, kamar su gonaki, da hasken rana, da taki mai ruwa, kafin su tsai da cewa, za su canja ire-iren shinkafa, tare kuma da kyautata hanyar samar da takin ruwa ga shinkafar da aka shuka. A karshe dai, sun samu sakamako mai faranta ran al'ummar kasar. Ya zuwa watan Oktoban shekarar 2016, an yi girbi a wata gonar gwaji dake filin yankin Imbo na lardin Bubanza dake kasar.

Irin shinkafa na kasar Sin da aka shuka yana da yawan gaske, domin kuwa har adadin sa da aka samu a gonar bisa alkaluma cikin ko wace hekta mai fadin 0.067 ya kai kilo 924, adadin da ya kai ninki sama da uku, idan aka kwatanta shi da na adadin da aka samu a sauran gonakin wurin.

Don haka ana iya cewa, adadin ya kafa tarihi a kasar ta Burundi, da ma fadin nahiyar Afirka. A wata gonar gwajin ta daban dake filin yankin na Imbo kuwa, ana iya ganin shinkafar da aka shuka nau'in kasar Sin na girma lami lafiya, kuma a bayyana take cewa, ta fi sauran shinkafar da manoman wurin suke shukawa inganci. Misali a fannin tsayi da kuma karfi.

Shugaban tawagar kwararrun aikin gona na kasar Sin ta uku, wanda shi ma ya kware sosai wajen aikin shuka shinkafa Yang Huade, ya yi mana bayani da cewa, "Wannan irin shinkafa yana da inganci, kuma ya dace a shuka shi a kasar ta Burundi, ga shinkafar da muka shuka a ranar 28 ga watan Satumban shekarar 2016, tana girma da kyau, an kuma yi hasashe cewa, adadin ta da za a samu a ko wace hekta 0.067 zai kai kilo 750 zuwa 800. Adadin da zai kai ninki biyu idan aka kwatanta shi da na adadin shinkafar da manoman wurin suke shukawa."

Wani manomin wurin Niligira Ferdinand, mai shekaru 45 da haihuwa, shi ma yana ganin cewa, shinkafar da ya shuka ba ta kai ingancin shinkafar da kwararrun kasar Sin suka shuka a gonar gwajin ba. Ya gaya mana cewa, "Akwai babban banbanci dake tsakanin wadannan gonaki biyu, dalilin da ya sa haka shi ne kwararru a fannin aikin gona na kasar Sin, na amfani da fasahar zamani, sabanin manoma na gida, wadanda ke amfani da fasahar shuka shinkafa ta da cana. Muna fatan za mu samu taimako daga wajensu."

Kwararrun aikin gonan kasar Sin su kan gudanar da aiki a cikin gonaki, saboda da haka za su iya warware matsala cikin lokaci, kuma suna ganin cewa, idan ana son kara shuka shinkafa mai inganci irin ta kasar Sin a kasar ta Burundi, wajibi ne a horas da manoman kasar. Kawo yanzu, kwararrun kasar Sin sun riga sun shirya kwas din horas da manoma kan fasahar shuka shinkafa guda biyu. Manoman da suka samu horaswa sun zarta 120. Yang Huade ya bayyana cewa, "Muhimmin aikinmu yanzu shi ne yada fasahar shuka shinkafa da iri na kasar Sin, domin cimma wannan buri, ya zama wajibi mu horas da wasu kwararru a fannin, kana mu kan bukaci sassan da abin ya shafa na kasar Burundi, da su aika da ma'aikatansu domin su yi aiki tare da mu, ta haka za mu iya koyar da su fasahohin mu yadda ya kamata."

Bisa alkaluman da asusun bada lamuni na duniya IMF ya fitar, an ce, a shekarar 2015, yawan GDP na kowanen mutumin kasar ta Burundi bai wuce dalar Amurka 306 kacal ba, kana al'ummar kasar wadanda ke fama da talauci sun kai kaso 70 bisa dari. Kasar tana kuma tana fama da karancin abinci da ya kai kaso 30 bisa dari. A hannu guda kasar Sin tana son ci gaba da samar da taimako, da goyon baya ga wannan kasa a fannin aikin gona, saboda sharuddan halittun kasar kamar su ruwa, da kasa da hasken rana, sun dace a shuka shinkafa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China