in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An daidaita rikicin siyasar kasar Gambia ta hanyar sulhu
2017-01-22 12:19:18 cri

A sanyin safiyar ranar Asabar, bisa agogon Gambia, tsohon shugaban kasar wanda ya ki mika mulki Yahya Jammeh ya yi jawabi a gidan telabijin din kasar, inda ya sanar da aniyarsa ta sauka daga karagar mulkin kasar, da niyyar ficewa daga kasarsa ta Gambia. Lamarin ya nuna cewa, an samu daidaita rikicin siyasar kasar ta hanyar sulhu.

Kafin haka, shugaban kasar Mauritania Mohamed Aziz da takwaransa na kasar Guinea, Alpha Conde, tare da manyan jami'an kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen dake yammacin Afirka ECOWAS, sun isa Banjul, fadar mulkin kasar Gambia, a tsakar ranar 20 ga wata, don sulhunta bangarorin kasar a karo na karshe. Bayan wasu sa'o'i da suka yi suna tattaunawa, an samu damar cimma matsaya, inda Jammeh ya sanar da mika mulki.

A cewar mista Jammeh, ya sauka daga mulkin kasar ne bisa radin kansa, kasancewar duk wata matsala da ake fuskanta, za a iya daidaita ta ta hanyar lumana.

A nashi bangaren, shugaban kasar Mauritania Mohamed Aziz ya shedawa manema labaru cewa, Jammeh ya hakura da mulki ne bisa sharadin tabbatar da tsaronsa da na iyalinsa. Ya ce zai kaura zuwa wata kasa ta daban dake nahiyar Afirka, kuma zai iya komawa Gambia duk lokacin da yake da bukatar yin hakan.

A ranar 1 ga watan Disambar 2016 ne aka gudanar da zaben shugaban kasar Gambia, inda Adama Barrow ya lashe zaben, kuma a ranar 19 ga watan nan ne ya kamata ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar. Sai dai Yahya Jammeh ya nuna kin amincewa da sakamakon zaben, mako guda bayan da farko ya amince da shan kaye a zaben. Irin kwan-gaba kwan-bayan da ya yi, ya sa aka samu barkewar rikicin siyasa a kasar ta Gambia.

A karkashin wannan yanayi ne, Adama Barrow, ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 19 ga wata, a ofishin jakadancin kasar Gambia dake kasar Senegal, inda jakadun kasashe masu zaunannun kujeru a kwamitin sulhu na MDD, da tawagar jakadun kungiyar kasashen tarayyar turai EU, da tawagar jakadun kungiyar AU, da wakilin kungiyar ECOWAS dukkansu suka halarci bikin rantsar da mista Barrow.

Ban da haka kuma, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri, inda ya bukaci Gambia da ta gudanar da aikin mika mulki cikin ruwan sanyi bisa doka da oda. Yayin da kungiyar AU ta ce ba za ta ci gaba da amincewa da Yahya Jammeh a matsayin shugaban kasar Gambiya ba daga ranar 19 ga wannan wata.

A nasu bagaren, mambobin kungiyar ECOWAS 5 da suka hada da Senegal, Najeriya, Ghana, Togo, da Mali sun tura sojoji zuwa kasar Gambia a ranar 19 ga wata, don tilasta wa Yahya Jammeh ya mika mulkin kasar. Duk wadannan matakan da gamayyar kasa da kasa suka dauka sun kai ga daidaita rikicin siyasar kasar Gambia ba tare da zub da jini ba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China