in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gabatar da jawabi a ofishin MDD a Geneva
2017-01-19 11:12:07 cri

A jiya Laraba ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci wani babban taro a ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Geneva na kasar Switzerland, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi mai lakabin "gina duniya mai dogaro da juna". A cikin jawabin, shugaba Xi ya yi bayani filla-filla game da ra'ayin gina wata al'umma dake da fa'ida ga kowa, da bada shawarar kara yin shawarwari da mu'amala gami da hada kai da juna, a kokarin gina duniya mai cikakken zaman lafiya da ci gaba.

Da misalin karfe shida na yammacin ranar Laraba agogon kasar Switzerland ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da rakiyar shugaban babban taron MDD karo na 71 Mista Peter Thomson gami da babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya shiga babban dakin taro na ofishin MDD da ke kasar.

A cikin jawabin da ya gabatar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan mutunta 'yancin kasashe daban-daban, da kokarin samarwa kasashe damammaki bisa adalci, inda ya ce:

"Akwai wani karin maganar kasar Sin dake cewa, mahakurci, mawadaci ne. Yin hakuri gami da bude kofa ga juna zai taimakawa kasashe daban-daban su inganta dangantakarsu ta diflomasiyya. Ya kamata mu nace ga bin tafarkin demokuradiyya tsakanin kasa da kasa, da yin watsi da babakeren da wata kasa ko wasu kasashen ke nunawa. Kasashe daban-daban su ne za su samar da makomar duniya, su ne za su kafa ka'idojin duniya, su ne za su shiga a dama da su a wajen tafiyar da harkokin duniya, su ne kuma za su amfana daga nasarorin da duniya ta samu baki daya."

Xi ya kara da cewa, kamata ya yi kasashe su nuna kwazo a fannoni da dama, ciki har da raya dangantakar abokantaka, da tabbatar da tsaro, da habaka tattalin arziki, da yin musanyar al'adu da sauransu. Xi ya ce:

"Ya zama dole mu rika yin shawarwari a tsakaninmu, a kokarin raya duniyar da za ta kasance mai cikakken zaman lafiya. Sa'an nan, mu zama tsintsiya madaurinki daya, a tabbatar da tsaro a ko'ina a duniya. Na uku, mu inganta hadin-gwiwar da za ta kawowa juna moriya, domin gina duniya mai wadata. Na hudu, ya zama tilas mu karfafa cudanya tsakanin juna, da gina duniya mai hakuri da juna. Na karshe, mu nace ga bin hanyar kiyaye muhalli, domin samar da muhalllin duniya mai tsafta."

Bugu da kari kuma, Xi Jinping ya kwatanta wani abu don yin karin haske game da ra'ayoyin da ya gabatar, inda ya ce:

"Wukar sojan Switzerland, wata aba ce da ta shahara a kasar dake jaddada tunanin nuna jajircewa. A karon farko da na samu wakar, na yi mamaki yadda bil-Adama ya tsara yadda take da amfani da dama. A ganina, idan za mu iya samarwa duniya a irin wannan wukar sojan Switzerland, hakika,duk wata matsalar da ta bijiro mana, za mu yi amfani da ruhin wukar don magance ta. Ina da imanin cewa, idan kasashen duniya suka nuna himma da kwazo, za mu iya samar da irin wannan wukar sojan Switzerland."

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya sake nanata manyan manufofin gwamnatin kasar Sin hudu, wadanda ko ta yaya gwamnatin Sin ba za ta canja su ba. Xi ya ce:

"Mutane da dama suna maida hankali kan manufofin gwamnatin kasar Sin, wadanda ke jawo bambancin ra'ayi da dama. Yau zan yi muku karin bayani kamar haka, na farko, Sin ba za ta canja kudurinta na wanzar da zaman lafiya a duniya ba, na biyu, Sin ba za ta canja kudurinta na neman ci gaba kafada da kafada ba, na uku, Sin ba za ta canja kudurinta na kulla zumunta tare da sauran kasashe ba, na hudu wato na karshe shi ne, Sin ba za ta canja kudurinta na goyon-bayan tunanin kasancewar bangarori daban-daban a duniya ba."

A karshe, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin na daya daga cikin kasashen membobin da suka kafa MDD, kuma ta bayar da gudummawa ga shawo kan wasu muhimman batutuwan duniya ta hanyar yin shawarwari, ciki har da batun nukiliyar Iran da batun Siriya. A nan gaba, Sin za ta ci gaba da marawa MDD baya ta yadda za ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa. Xi ya ce:

"Kasar Sin za ta kare tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin MDD, da girmama muhimman ka'idojin raya dangantakar kasa da kasa, da kuma kiyaye mutunci gami da martabar MDD, da kuma mara baya ga MDD ta yadda za ta taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya. A halin yanzu, asusun neman zaman lafiya da ci gaba na Sin da MDD ya fara aiki, kuma Sin za ta maida hankali wajen zuba kudi a cikin ayyukan neman zaman lafiya da ci gaba da MDD gami da hukumomin kasa da kasa dake Geneva suka fitar."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China