in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ladsous ya yi Allah wadai da harin da aka kai a kasar Mali
2017-01-19 10:33:56 cri

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da shirin wanzar da zaman lafiya Herve Ladsous ya yi Allah wadai da harin kunar bakin waken da aka kaiwa sansanin sojojin MDD da ke kasar Mali.

Jami'in na MDD ya bayyana cewa, harin na ranar Laraba tamkar yunkurin mayar da hannun agogo baya ne a kokarin da majalisar ke yi na wanzar da zaman lafiya a kasar.

Ladsous ya shaidawa taron kwamitin sulhun MDD cewa, harin da aka kai da bam a yankin Goa na kasar ta Mali ya sabbaba mutuwar a kallo sojoji 50, tare da jikkata wasu kimanin 60.

A ranar 15 ga watan Mayun shekarar 2015 ne manyan kungiyoyin 'yan tawayen da ke arewacin kasar, ban da kungiyar Azwad suka sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da sansantawa tare da kungiyoyin masu dauke da makamai da ke goyon bayan gwamnati gami da wasu kananan kungiyoyin 'yan tawaye da ke kasar.

Daga bisani kuma kungiyar CMA ta sanya hannu a kan wannan yarjejeniya a birnin Bamakon kasar Mali, matakin da ya kawo karshen sanya hannu cimma wannan yarjejeniya da nufin kawo karshen tashin hankali a kasar, da kuma bullo da shirye-shiryen raya yankin arewacin kasar da ke fama da tashin hankali, da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China