in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya gabatar da jawabi a taron shekara shekara na dandalin tattalin arzikin duniya
2017-01-18 12:10:46 cri


Jiya Talata da safe, agogon kasar Swiszerland ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shekara shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na shekarar 2017, yayin bikin bude taron, shugaba Xi ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen duniya su yi kokari tare domin bullo da wani sabon nau'i na ci gaban tattalin arziki.

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, "Yau, bari in fara da batun samun ci gaban tattalin arziki tare a fadin duniya, ina so in nuna muku matsayina game da tattalin arzikin duniya."

Shugaba Xi ya fara jawabinsa ne da batun ci gaban tattalin arziki wanda ya fi jawo hankalin al'ummomin duniya, yana mai cewa, a halin da ake ciki yanzu, ba a samu ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata ba, kasashe masu ci gaba, ko kasashe masu tasowa, dukkansu suna fuskantar matsin lamba, a saboda haka, kamata ya yi a kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa, ta yadda kowa da kowa a duniya zai amfana da ci gaban tattalin arziki. Shugaba Xi yana mai cewa, "Tattalin arzikin duniya ya shafi kowa da kowa, ko kana mai da hankali a kan shi, ko a'a, babu wani banbanci, kuma tattalin arzikin duniya tamkar teku ne, daukacin kasashen duniya suna cikin wannan teku, ba zai yiwu wata kasa ta samu ci gaban tattalin arziki ita kadai ba."

Shugaba Xi yana ganin cewa, yanzu abu mafi muhimmanci shi ne a kara kokari tare domin kubutar da tattalin arzikin duniya daga mawuyacin halin da yake ciki. A game da batun yadda za a warware matsalar, ya bayyana cewa, wajibi ne kasashen duniya su hada kai domin bullo da wani sabon nau'i na hadin gwiwa a tsakaninsu. Yana mai cewa, "Za mu nace ga manufar raya tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, wannan zai sa kasashen duniya su amfana da ci gaban tattalin arziki. Kuma muddin ana bukatar a tabbatar da wannan burin, ya kamata kasashen duniya su kara karfafa cudanya da taimakon juna, ta yadda a karshe za a samu wadata tare. Bugu da kari, ya kamata mu kara bunkasa ciniki maras shinge da zuba jari a fadin duniya, tare kuma da yaki da manufar ba da kariya ga cinikayya."

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya sake yin bayani kan manufofin neman samun ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, inda ya jaddada cewa, al'ummar kasar Sin sun gano sosai cewa, idan ana son samun ci gaba, dole ne a yi kokari matuka a ko da yaushe. Ya ce, kasar Sin babbar kasa ce mai yawan al'umma, wanda adadinsu ya kai biliyan 1 da miliyan 300, dole ne ta samu ci gaba ta hanyar dogaro da kanta, yanzu da gaske kasar Sin ta bunkasa cikin sauri, amma kafin a yaba da sakamakon da ta samu, dole ne a duba kokarin da take yi, da kuma alherin da take samarwa kasashen duniya. Yana mai cewa, "Ci gaban kasar Sin zai samar da damammaki ga sauran kasashen duniya, kasar Sin tana cin gajiyar ci gaban tattalin arzikin duniya, a sa'i daya kuma, tana kawo moriya ga sauran kasashen duniya, al'ummar kasar Sin sun fahimci wahalhalun da ake sha yayin da ake kokarin samun wadata, shi ya sa su kan yaba da sakamakon da sauran kasashen duniya suka samu, kuma su kan nuna fatan alheri gare su, haka kuma ba sa nuna musu kishi, suna kuma fatan sauran kasashe za su samu moriya daga ci gaban kasar Sin."

Kana shugaba Xi ya bayyana cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara mai da hankali kan ingancin karuwar tattalin arziki, tare kuma da kara kyautata muhallin zuba jari, ta yadda za ta samar da tsarin bude kofa na gari ga kasashen waje. Shugaban ya fayyace cewa, kasar Sin za ta shirya taron koli game da hadin gwiwar kasa da kasa na "ziri daya da hanya daya" a nan birnin Beijing a watan Mayu mai zuwa, domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da ake fuskanta yayin da ake kokarin raya tattalin arzikin shiyya shiyya da na duniya.

Shugaban dandalin tattalin arzikin duniya Klaus Schwab ya bayyana cewa, halartar dandalin da shugaba Xi ya yi, tana da muhimmanci matuka a tarihi, ba ma kawai ta yada muhimman bayanai ga kasashen duniya ba, har ma ta kara karfafa zukatan al'ummomin kasashen duniya. Yana mai cewa, "Duniyar da muke ci, duniya ce mai dogaro da juna, bai kamata ba a kafa shinge tsakanin kasa da kasa, kamata ya yi a samu ci gaba tare, bil adama suna da makoma guda, shi ya sa alkawarin da kasar Sin ta dauka wato samun ci gaba tare yana da muhimmanci matuka. Na san burin kasar Sin, ina ganin cewa, burin kasar Sin da burin duniya, iri daya ne, saboda haka, ya kamata mu hada kai domin cimma burin da muka sanya a gaba."

Taken dandalin tattalin arzikin duniya na bana shi ne "karfin ba da jagoranci: hada kai tare da sauke nauyi da ke kanmu." Shugabannin kasashe da gwamnatoci kusan 50 da wakilan fannonin siyasa da masana'antu da kasuwanci da masana da kafofin watsa labarai 1700 suka halarci bikin bude taron.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China