in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya kara hasashensa game da ci gaban tattalin arzikin Sin a bana
2017-01-17 12:37:07 cri

Jiya Litinin, asusun bada lamuni na duniya IMF ya fitar da wani sabon rahoton hasashensa game da bunkasar tattalin arzikin duniya, inda ya kara hasashen da yake yi game da ci gaban tattalin arzikin kasashen Sin da Amurka a bana. A waje daya kuma, rahoton ya ce, sauye-sauyen da ake tunanin samu a manufar sabuwar gwamnatin Amurka, ka iya haifar da rashin tabbas ga tattalin arzikin duniya a nan gaba. Haka kuma a cewar rahoton, ci gaban tattalin arzikin duniya, batu ne da zai shafi dukkanin fannoni da kasashe.

A wajen wani taron manema labarai da aka yi jiya, babban masanin tattalin arziki na IMF Maurice Obstfeld ya bayyana cewa, bayan da duniya ta yi fama da tawayar tattalin arziki a shekarar da ta shude, tattalin arzikin duniya zai kara bunkasa cikin sauri a bana da kuma badi. Mista Obstfeld ya ce:

"Idan aka kwatanta hasashen da muka yi a watan Octoban bara, a halin yanzu muna ganin cewa, za mu kara hasashen da muke yi game da ci gaban tattalin arzikin Amurka, Sin, Turai, da kuma Japan."

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya kara hasashen da yake game da karuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana wanda ya kai kashi 6.5 bisa dari. Mista Obstfeld ya yi bayani kan dalilin haka, inda ya ce:

"A cikin sabbin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasu cikin sauri, Sin ta zama babbar kasa dake taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya. Mun kara hasashen da muka yi game da bunkasar tattalin arzikin Sin a bana, saboda mun gano cewa Sin ce babban ginshikin farfadowar tattalin arzikin fadin duniya a bana."

Amma rahoton ya yi nuni da cewa, kamata ya yi gwamnatin kasar Sin ta dauki wasu matakai na rage karuwar basussukan da take bayarwa, da kuma magance matsalar basussuka da kamfanoni ke fuskanta.

Bugu da kari, sakamakon kara kudin ruwan da baitulmalin Amurka ya yi, asusun IMF ya rage hasashen da ya yi kan saurin bunkasuwar tattalin arzikin wasu kasashe a bana, ciki har da Indiya, Brazil da Mexico.

A waje daya kuma, IMF ya kara hasashen da yake yi kan ci gaban tattalin arzikin kasar Amurka a bana da badi, sakamakon wasu manufofin da gwamnatin kasar ta dauka, na habaka tattalin arziki gami da rage harajin da za'a biya. Amma rahoton IMF ya ce, akwai abubuwa na rashin tabbas da dama game da hasashen da yayi kan ci gaban tattalin arzikin Amurka. Mista Obstfeld ya kara hasken cewar, idan kasashe daban-daban suka nuna kiyayya ga juna lokacin da suke gudanar da harkokin cinikayya tsakaninsu, hakan na iya haifar da illa ga tattalin arzikin duniya, inda ya ce:

"Yiwuwar samun matsaloli a cinikayya ka iya kawo koma-bayan tattalin arzikin duniya. Muna tunanin cewa, a nan gaba kasashe za su san cewa wadannan matakai ba na son kai ba ne, musamman idan aka samu barazanar ramuwar gayya daga wasu kasashe. A bangare guda, wannan zai iya faruwa saboda matsalolin cinikayya, inda dukkan kasashe za su fuskanci koma baya."

A takaice dai, wannan sabon rahoton da asusun IMF ya fitar, ya kara bada tabbacin cewa tattalin arzikin kasashe masu sukuni zai karu a nan gaba, amma ya yi taka-tsantsan game da ci gaban tattalin arziki na kasashen dake tasowa a fadin duniya. Mista Obstfeld ya sake jaddada cewa, lokacin da ake fuskantar sauye-sauyen tattalin arzikin duniya, ya zama dole a kara maida hankali kan raya tattalin arzikin da zai shafi kowace kasa da kowane fanni. Mista Obstfeld ya ce:

"Dinkuwar duniya waje daya, gami da sauye-sauyen da ake fuskanta a fannin kimiyya da fasana, za su haifar da rashin adalci a tsakanin al'umma, al'amarin da zai dada kamari nan gaba, kuma hakan zai janyo rashin nuna adalci da rashin biyan albashin ma'aikata a kasashe da dama. Ranar 16 ga watan da muke ciki, rana ce da aka kebe don tunawa da marigayi Martin Luther King, wato babban mai fafutukar kare hakkin bil'adama a Amurka. Ya kamata mu amince da irin bayanin da muka yi a bara, wato ci gaban tattalin arziki mai dorewa, ci gaba ne wanda ya shafi kowace kasa gami da kowane fanni."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China