in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya fara ziyararsa ta farko a bana a Swiszerland
2017-01-16 10:22:34 cri

A jiya Lahadi 15 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar aiki a kasar Swiszerland, daga bisani kuma zai halarci taron shekara shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na Dawos na shekarar 2017, da kuma wasu hukumomin kasa da kasa dake kasar.

A jiya da rana, agogon kasar Swiszerland ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargida Peng Liyuan suka sauka a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na birnin Zurich cikin jirgin sama na musamman, inda shugabar tarayyar kasar Doris Leuthard da maigidanta suka shirya gagarumin bikin maraba da zuwansu, daga baya ne kuma shugabannin kasashen biyu suka shiga jirgin kasa na musamman na gwamnatin kasar ta Swiszerland domin zuwa Bern, fadar mulkin kasar. A yayin bikin da aka shirya masa a babban ginin tarayyar kasar, shugaba Xi ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana cewa, "Makasudin ziyarata a Swiszerland shi ne domin kara karfafa zumuncin da hadin gwiwa dake tsakaninmu. Ina fatan Sin da Swiszerland za su tattauna a kan fannoni daban daban dake shafar hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu domin ciyar da huldar abokantaka dake tsakanin Sin da Swiszerland gaba yadda ya kamata."

Ziyarar aiki ta farko da shugaba Xi ke gudanarwar a Swiszerland ta jawo hankalin jama'a a fadin duniya, inda rahotanni ke nuna cewa, yayin ziyarar, sassan biyu za su daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama, misali a fannonin siyasa, da ciniki maras shinge, da al'adu, da kwastan, da makamashi, da wasannin motsa jiki da dai sauransu, kana sassan za su kara habaka hadin gwiwa dake tsakaninsu a fannin yawon bude ido, lamarin da zai kawo moriya ga al'ummomin kasashen biyu.

Bayan kammala ziyara a birnin Bern, shugaba Xi zai halarci taron shekara shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na Dawos na shekarar 2017, kuma zai gabatar da muhimmin jawabi a yayin bikin bude taron da za a shirya a gobe, 17 ga wata, inda zai yi bayani game da matsayin kasar Sin kan yadda za a kubutar da kasashen duniya daga mawuyacin halin tabarbarewar tattalin arziki.

Mataimakin shugaban cibiyar nazarin batutuwan kasa da kasa ta kasar Sin Ruan Zongze ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin zai halarci dandalin tattalin arzikin duniya, lamarin ya jawo hankalin jama'a matuka. Yana mai cewa, "Yanzu kasashen duniya suna fama da tabarbarewar tattalin arziki, kuma wasu kasashe ba su samu ci gaba kamar sauran kasashen duniya ba, kana wasu sun nuna ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, ban da haka kuma, a duk shekara dandalin Dawos ya kan taka muhimmiyar rawa wajen ba da jagora ga makomar ci gaban tattalin arziki, shi ya sa shugaba Xi zai bayyana ra'ayin kasar Sin a dandalin, ko shakka babu hakan zai kara karfafa zuciyar al'ummomin kasashen duniya."

Kazalika, yayin da ya ke ziyara a kasar ta Swiszerland, shugaba Xi Jinping zai ziyarci ofishin MDD dake Geneva, inda zai gabatar da wani muhimmin jawabi a fadar "Palace of Nations" domin nuna ra'ayin kasar Sin kan yanayin da kasashen duniya ke ciki, da tsarin kasa da kasa, tare kuma da jaddada muhummancin makomar bil adama. A cikin jawabin da zai gabatar, shugaba Xi zai bayyana manufofin kasar Sin game da samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya, da kiyaye ka'idojin MDD. Ruan Zingze ya bayyana cewa, hakkin MDD ya tabbatar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, kuma shugaba Xi zai bayyana matsayin kasar Sin a ofishin MDD, matakin da ake fatan zai taimaka wa shirin kasar Sin ya samu karbuwa a wajen al'ummomin kasashen duniya. Yana mai cewa, "Shirin kasar Sin da matsayin kasar Sin game da harkokin duniya karin hasken ne game da manufofin tafiyar da harkokin gidan kasar Sin, wato manufofi ne da za su dace a aiwatar da su yayin da ake gudanar da harkokin duniya, misali, sabon nau'in huldar dake tsakanin kasashen duniya da makomar bil adama, ina ganin cewa, wadannan ra'ayoyi sun sha bambam da tsoffin ra'ayoyi na koma baya da ake amfani da su a baya, misali, a yi galaba a kanka, ko ka yi galaba a kan wasu, ba zai yiwu a samu ci gaba tare ba. Duk da cewa, zai yi wahala a amince da wadannan ra'ayoyi na kasar Sin, amma duk da haka, akwai bukatar a kara kokari, kuma wajibi ne a gabatar da sabbin ra'ayoyi, domin nan gaba za a kara fahimtar tasiri da ma'anar kokarin da kasar Sin take yi yanzu."

Yayin ziyarar tasa, shugaba Xi zai ziyarci hedkwatar hukumar lafiya ta duniya WHO da hedkwatar kwamitin wasannin Olympic na duniya, ana sa ran cewa, ziyarar za ta taimaka wajen kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China