in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sauyin yanayi da ake samu kan hadin gwiwar Sin da Afirka
2017-01-13 12:35:05 cri

Kwanakin baya, ministan harkokin wajen kasar Sin mista Wang Yi ya kai ziyara a wasu kasashen dake nahiyar Afirka, da suka hada da Madagascar, Zambia, Tanzania, Jamhuriyar Congo, gami da Tarayyar Najeriya. Wannan ziyara ta sa ana tunanin yadda ake aiwatar da matakan da aka tanada, a babban taron shugabanni da ya gudana a Johannesburg a shekarar 2015, karkashin laimar dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, inda ake ganin sauyin da ake samu a yanayin da ake ciki dangane da batun.

A sabili da wasu sabbin ra'ayoyin da aka amincewa a yayin taron Johannesburg, an fara ganin sauyawar yanayi a fannoni uku, dangane da batun hadin gwiwar Sin da Afirka. Na farko shi ne, a da an fi gudanar da ayyukan hadin kai bisa matakan da gwamnatocin bangarorin 2 suka dauka, amma yanzu ana dogaro kan 'yan kasuwa masu zaman kansu. Na biyu kuwa, shi ne an fi mai da hankali kan cinikayya a baya, amma yanzu an karkata ga hadin gwiwa ta fuskar masana'antu. Sa'an nan na uku shi ne, a baya kamfanonin Sin suna gudanar da ayyukan kwangila ne kawai, amma yanzu suna zuba jari, suna daukar nauyin gina wasu ayyuka, haka kuma suna kula da kayayyakin da aka gina don samar da hidima.

Ta wadannan sauye sauye, za a iya ganin cewa hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka na samun ci gaba, daga fannonin akidar da ake bi, da tsare-tsaren ayyuka, gami da bangarorin da suke gudanar da aikin.

Yanzu ana iya cewa, an dauki takamaiman matakai don cika alkawaran da aka yi, da yarjeniyoyin da aka kulla wajen taron Johannesburg. Da ma a wajen taron, bangaren Sin ya sanar da wasu manyan shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10, don taimakawa raya masana'antun kasashen Afirka, da zamanintar da aikin gona a nahiyar, haka kuma ta yi shirin ware dalar Amurka biliyan 60 don gudanar da wannan aikin.

Yanzu haka bisa kididdigar da aka yi, zuwa watan Yulin bara, kasar Sin da wasu kasashen dake nahiyar Afirka, sun riga sun kulla yarjeniyoyin da kudinsu ya zarce dalar Amurka biliyan 50. Ban da haka kuma ana kokarin gina wasu manyan kayayyakin more rayuwa, da yankunan tattalin arziki da na masana'antu, har ma an riga an kammala gina wasu, an kuma fara amfani da su. Ta haka, ana iya ganin alamar ci gaba ta fuskar hadin gwiwar Sin da Afirka.

A shekarar 2016, an kammala wasu manyan ayyuka karkarshin tsarin hadin kan Sin da Afirka, lamarin da ya janyo hankalin jama'ar kasashe daban daban. A gabashin Afirka, an gina layin dogo na zamani da ya hada Adis Abeba da Djibouti, inda aka yi amfani da kimiyyar kasar Sin, da kayayyakin kirar kasar Sin wajen shimfida layin, wanda ya kasance irinsa na farko da aka gina a nahiyar Afirka.

A yammacin nahiyar kuwa, an fara amfani da layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna a Tarayyar Najeriya, wanda shi ma wani kamfanin kasar Sin ne ya dauki nauyin gina shi. Sa'an nan a shekarar da muke ciki, za a yi gwajin aiki da layin dogon da ya hada birnin Nairobi da tashar teku mafi girma a gabashin Afirka ta Mombasa. Duk wadannan kayayyakin more rayuwa za su iya taimakawa raya tattalin arzikin kasashen da suke ciki, gami da sa kaimi ga dunkulewar tattalin arzikin yankuna daban daban.

Ban da haka kuma, an ce kasar Sin da kasashen Zambia da Tanzania, za su yi hadin gwiwa, wajen aiwatar da kwaskwarima kan layin dogon da ya hada Tanzania da Zambia, wanda ke da ma'anar tarihi, musamman ma wajen alamantar abokantakar da ke tsakanin Sin da Afirka. Za a daidaita tsarin kula da layin dogon, da hada shi da tashar teku, gami da kafa zirin tattalin arziki a dab da layin, ta yadda za a samu damar kyautata tsarin layin dogon, don taimakawa ci gaban tattalin arzikin kasashen Zambia da Tanzania da sauran kasashen dake dab da layin.

A wani bangare na daban kuma, kasar Sin tana kokarin taimakawa Jamhuriyar Congo wajen raya yankin tattalin arziki na musamman na Pointe-Noire, don ya zama wata shaida ga hadin kan Sin da Afirka a fannin masana'antu. An ce za a raya masana'antu na zamani a yankin, wanda zai taimakawa aikin jigilar kaya, da fannin samar da kayayyaki, da zirga-zirgar jiragen sama, da dai sauransu.

A nasa bangare, shirin "Ziri Daya da Hanya Daya", bisa matsayinsa na wani babban shirin hadin gwiwa da kasar Sin ta gabatarwa duniya, yana samar da dama ga hadin kan Sin da Afirka. A halin yanzu, kasar Sin na karfafa wa Madagascar gwiwarta, don ta yi amfani da fifikon da take da shi a fannin wurin da take, da albarkatunta, ta yadda za ta iya kasancewa gadar da za ta hada "ziri daya da hanya daya" da ake kokarin ginawa da nahiyar ta Afirka. Wannan shirin shi ma ya zama damar raya tattalin arziki da kyautata kayayyakin more rayuwar jama'a ga kasar Mardagascar, a cewar wasu jami'an gwamnatin kasar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China