in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan manufofinta na hadin kan tsaro a yankin Asiya da tekun Pasifik
2017-01-12 11:06:21 cri

A jiya Laraba ne ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani karo na farko kan manufofinta, na gudanar da hadin kai game da tsaron yankin Asiya da tekun Pasifik. Wani babban jami'in gwamnatin kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta dauki wannan mataki ne bisa fatan dukkan bangarorin da abin ya shafa, za su kara fahimtar manufofin gudanar da hadin kan tsaro a yankin Asiya da tekun Pasifik da kasar Sin ke bi. Sannan kasar Sin tana kuma fatan ita da sauran kasashen dake yankin, za su iya kokari tare, ta yadda za su iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin cikin hadin gwiwa, a kokarin bunkasa yankin Asiya da tekun Pasifik tare.

Wannan takardar "manufofi na kasar Sin kan hadin kan tsaro a yankin Asiya da Pasifik" tana kunshe da kalmomi dubu 16 ko fiye, a cikinta an bayyana manufofi, da ra'ayoyi, da tunanin kasar Sin, don gane da gudanar da hadin kan tsaron yankin Asiya da tekun Pasifik, da kuma dangantakar dake tsakanin kasar Sin da wasu muhimman kasashen da ke yankin, da matsayin da take dauka kan wasu batutuwa masu jawo hankulan mutane.

A yayin taron fitar da wannan takarda da aka shirya jiya Laraba, kakakin ofishin yada labaru na majalissar gudanarwa ta kasar Sin Mr. Hu Kaihong, ya bayyana cewa, "A 'yan shekarun nan, yankin Asiya da tekun Pasifik inda aka samu bukasuwa sosai yana ta jawo hankulan sauran kasashen duniya sosai, ya kuma zama yankin da aka fi samun karfin samun ci gaba. A kullum Kasar Sin na kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da neman bunkasa a yankin. Kuma tana tsayawa tsayin daka kan matsayin neman ci gaba cikin lumana, da manufar bude kofarta ga duk duniya domin neman samun nasara tare. Sannan tana tsayawa tsayin daka kan matsayin bunkasa dangantakar sada zumunta irin ta hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya, bisa ka'idoji biyar na zaman tare cikin lumana. Kaza lika tana gudanar da hadin gwiwa da sauran kasashen yankin a dukkanin fannoni."

A cikin 'yan shekarun nan, musamman a shekarar 2016, sauye-sauyen halin siyasa da tattalin arziki da aka samu masu sarkakiya a duk duniya sun ja hankula sosai. A wannan halin da ake ciki yanzu, yankin Asiya da tekun Pasifik yana ta samun bunkasa. Mr. Liu Zhenmin, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, an samu wannan ci gaba ne sakamakon hadin gwiwar da ake yi sosai a tsakanin kasashen yankin. Ya jaddada cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ta fitar da wannan takarda a farkon shekarar 2017, shi ne tana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa, za su kara fahimtar manufofinta na yin hadin kai game da tsaro a yankin Asiya da tekun Pasifik, tana kuma fatan za a mayar da martani cikin yakini, a kokarin kara yin hadin gwiwa wajen tsaron yankin, ta yadda za su iya bayar da karin gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

A matsayin muhimman kasashe biyu dake yankin, ana mai da hankali sosai kan kowane irin canji na dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Lokacin da yake ba da amsa ga tambayar da aka yi masa cewa, ko kasar Sin tana son maye gurbin kasar Amurka a yankin Asiya da tekun Pasifik? Mr. Liu Zhenmin ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ake yi tsakanin wadannan kungiyoyin tattalin arziki biyu, na da matukar muhimmanci ga tsaron yankin Asiya da tekun Pasifik. Sakamakon haka, ana bukatar kasashe daban daban, musamman manyan kasashen dake yankin su yi kokari tare wajen tsaron yankin. Ko da yake kasar Amurka kasa ce mafi karfi a duk duniya, amma ita kadai ba za ta iya tsaron yankin Asiya da tekun Pasifik kamar yadda ake fata ba. Kuma kasar Sin ba ta da sha'awar maye gurbin Amurka a yankin Asiya da tekun Pasifik. A waje daya, ya ambaci dangantakar dake tsakanin Sin da sauran kasashen duniya. Liu Zhenmin ya ce, "Kasar Sin na kokarin magance tada hankali, ko nuna adawa ga kasar Amurka. Tana kuma fatan kasashen biyu za su girmama juna, da yin hadin gwiwa domin neman nasara tare. Sannan kasar Sin na kokarin karfafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni a tsakaninta da kasar Rasha. Bugu da kari, kasar Sin tana kokarin kara bunkasa dangantakar abokantaka da kasar Indiya, domin neman ci gaba cikin hadin gwiwa. A waje daya, kasar Sin na tsayawa kan matsayinta na sada zumunta da kasashe makwabta, domin zurfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da kasashe makwabta."

A shekarar da ta gabata, halin da ake ciki a yankin tekun kudancin Sin ya jawo hankalin mutane sosai. Liu Zhenmin ya ce, kasar Sin tana da imanin cewa, kasashen da ke kewayen yankin tekun kudancin Sin, za su samu sabon ci gaba a fannin hadin kai a batun tekun a shekarar 2017.

Kasar Sin wata muhimmiyar mamba ce a yankin Asiya da tekun Pasifik. Ko za a iya samun bunkasa da dauwamammen tsaron kai a yankin, hakan yana da alaka sosai da makomar kasar Sin, da alherin al'ummar Sinawa. Shugaban sashen nazarin yankin Asiya da tekun Pasifik na hukumar nazarin batutuwan duniya ta kasar Sin Mr. Liu Qing ya bayyana cewa, "A 'yan shekarun nan, wasu kafofin yada labaru sun bayyana cewa, kasar Sin ba ta bayyana manufofinta na tsaron kai a bayyane ko a fili ba. Sakamakon haka, ba a fahimtar manufofin kasar ta Sin game da tsaron kai ba, har ma wasu na nuna shakku game da manufofin tsaron kai na kasar Sin. Kasar Sin ta fitar da wannan takardar bayani ta manufofin gudanar da hadin kai na tsaron yankin Asiya da Pasifik' a yanzu ne, domin ta bayyana manufofinta daga dukkan fannoni, wannan zai taka rawa kan yadda sauran kasashen duniya ke fahimtar ra'ayoyin kasar Sin na tsaron yanki." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China