in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai kai ziyararsa ta farko a shekarar 2017
2017-01-11 19:53:31 cri

A ranar 15 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki kasar Switzerland, kuma wannan shi ne karo na farko da ya kai ziyara ketare a bana. Ana saran a yayin wannan ziyara, shugaba Xi zai halarci taron shekara shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya (WEF) na shekarar 2017 a birnin Davos na kasar Switzerland, tare kuma da ziyartar ofishin MDD dake Geneva da hedkwatar hukumar lafiya ta duniya WHO da kuma hedkwatar kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya. Game da wannan batu, mataimakin ministan harkokin wajen Sin, Li Baodong ya bayyana wa 'yan jarida na Sin da na ketare cewa, ziyarar shugaba Xi za ta bude wani sabon babi a harkokin diplomasiyyar Sin a bana. Kuma taron WEF da shugaba Xi zai halarta, yana da matukar muhimmanci a tarihi. 

Kasar Switzerland, tana daga cikin kasashen yammacin duniya da suka amince da matsayin Jamhuriyyar jama'ar kasar Sin, kuma daga ckin kasashen da suka fara kulla huldar diplomasiya da Sin. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, Sin da Switzerland suna raya dangantaka tsakaninsu lami lafiya, tare da samun babban sakamako a hakikanin hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannoni daban daban. Wannan ne karo na farko da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara a kasar tun shekarar 2000. Ko da yake ziyarar ce ta kwanaki hudu kawai, amma an shirya abubuwa masu dimbin yawa da shugaban zai gudanar a lokacin wannan ziyara, ciki har da ganawa a tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da halartar taron WEF, da kuma ziyartar kungiyoyin duniya da dama.

Mista Li ya bayyana cewa, a birnin Berne, hedkwatar kasar Switzerland, shugaba Xi zai yi musayar ra'ayi da shugabannin kasar game da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da hanyoyin da kasashen biyu za su bi, da manufofinsu na gida da na waje, da kuma harkokin duniya da na shiyya shiyya da suka fi jawo hankulansu, domin kara amincewa da juna, da samar da makoma mai kyau ga kasashen biyu. Bangarorin biyu za su daddale yarjeniyoyi a fannonin siyasa, da cinikayya cikin 'yanci, da makamashi da sauransu. Li ya kara da cewa, (1)

"Karfafa mu'amala tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin samar da sabbin kayayyaki da cinikayya cikin 'yanci da sauransu, ba ma kawai kasashen biyu za su samu moriyar juna da kawo alheri ga jama'arsu ba, har ma zai share fagen dangantakar siyasa cikin yakini a tsakanin kasashen duniya, wadda ta nuna cewa, Sin da Switzerland za su hada kai tare domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da kiyaye tsarin cinikayya cikin 'yanci a duniya da bude kofa, domin sa kaimi ga tsarin kulawa da kasashen duniya zuwa wani sabon mataki mai dacewa."

A ranar 17 ga wata ne, za a kaddamar da taron shekara shekara na dandalin tattaunawar tattalin arziki a duniya a Davos. Taken taron na bana shi ne "Karfin yin ja-gora: Gudanar da harkoki bisa yanayin da ake ciki, da daukar alhaki yadda ya kamata", da zummar yin kira ga shugabannin sassa daban daban domin kara kwarin gwiwar jama'a kan makomar bunkasuwar duniya. Shugaba Xi zai yi jawabi a yayin bikin bude taron. Mista Li ya bayyana cewa, (2)

"Shugaba Xi zai bayyana ra'ayin Sin dangane da harkokin tattalin arzikin da ke jawo hankalin kasa da kasa, da sa kaimi ga ra'ayoyin bangarori daban daban kan wannan batu, da yin kokarin jagorantar dunkulewar tattalin arzikin duniya cikin hakuri da samun moriyar juna. Haka kuma zai yi nazari kan manyan dalilan da suka haddasa mawuyacin halin da ake fuskanta wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, da neman hanyoyin daidaita wannan batu. Bugu da kari. Ban da haka, shugaba Xi zai kuma bayyana sakamakon da aka samu a fannin yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje da fasahohin da kasar Sin ta samu, ta yadda kasashen duniya za su kara fahimtar yanayin tattalin arzikin Sin yadda ya kamata."

Ban da haka, a ranar 18 ga wata, shugaba Xi zai kai ziyara ofishin MDD dake Geneva, da hukumar lafiya ta duniya WHO, da kuma hedkwatar kwamitin shirya gasar wasannin Olympics bisa goron gayyatar shugabanninsu bi da bi. Li Baodong ya bayyana cewa, (3)

"Shugaba Xi zai gabatar da jawabi mai taken 'Kafa tarayyar kaddarar da bil'adam' a hedkwatar MDD, inda zai gabatar da ra'ayin Sin game da harkokin da suka fi jawo hankalin kowa da kowa, da yin musayar ra'ayi da shugabannin MDD, domin daga matsayin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, da kuma zurfafa hakikanin hadin gwiwa tsakanin Sin da kungiyar WHO da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics." (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China